Tunawa da haɗarin jirgin saman Alhazai a Kano 1973

0
105

A cikin watan da ya gabata ne (watan Janairu 1973) Wani jirgi ƙirar Boeing 707 da aka yi hayarsa ya kama da wuta lokacin da ya ke sauƙa a filin jirgin saman Kano, Najeriya, in da ya kashe mutane 176 da ke cikinsa.

Haɗarin jirgin saman na Kano ya kasance jirgin fasinja Boeing (707) da aka yi haya a ranar (22) ga watan Janairun shekara ta alif (1973) wanda ya yi haɗari yayin da yake ƙoƙarin sauƙa a Filin jirgin saman Kano. Wannan shi ne haɗari mafi girma na jirgin sama da ya taɓa faruwa a Najeriya, yayin da fasinjoji (176) da ma’aikata suka halaka a cikin haɗarin.

Akwai mutane 22 da suka tsira. Wannan da ya haɗa da matuƙin jirgin da ma’aikatan jirgin, bisa ga rahoton New York Times.

KU KUMA KARANTA:Birnin Almaty, birnin da ya shahara da yawan tsirrai na Tufafi a Kazakhstan

Wannan shi ne haɗarin jirgi mafi tayar da hankali zuwa lokacin. Gabanin 1973, jirgin ƙasar Rasha ne ya taɓa haɗari inda mutane 176 suka hallaka. Jirgin mahajjatan mai ƙirar Boeing 707, mallakan ƙasar Jordan na ɗaya daga cikin jiragen da ke jigilar mahajjatan Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya a lokacin.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya kama da wuta ne yayinda ya nufi filin jirgin saman Kano. Amma dai ba a tabbata ko jirgin ya taɓa ƙasa ba a lokacin.

Leave a Reply