‘Yan bindiga sun kashe ‘yansanda da garkuwa da mutane 40 a Zamfara

0
88

Daga Ibraheem El-Tafseer

Masu garkuwa da mutane sun kashe ‘yansanda biyu da wasu fararen hula tare da garkuwa da mutane kimanin 40 a ƙauyen Kasuwar-Daji da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar Zamfara.

Wani mazaunin ƙauyen ya tabbatar wa BBC cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da sanyin safiyar yau Talata inda suka riƙa yin harbin mai-uwa-da-wabi.

Hakan na zuwa ne kimanin mako biyu bayan da gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare ya ƙaddamar da rundunar Askarawan Zamfara, waɗanda za su taimaka wajen yaƙi da matsalar tsaron da jihar ke fuskanta.

Zamfara na daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro, inda ‘yan bindiga ke far wa ƙauyuka suna kashewa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

KU KUMA KARANTA: Ina cikin waɗanda ƴan bindiga ke son kai wa hari — Dikko Radda

Gwamnatin Tarayya, wadda ita ce kundin tsarin mulki ya ɗora wa alhakin tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar, na cewa tana ɗaukan matakan da suka kamata wajen shawo kan lamarin.

A tattaunawarsa da BBC cikin kwanakin baya, ƙaramin minstan tsaro na Najeriya Bello Matawalle ya ce ana ɗaukar matakan kawar da matsalar baki ɗaya.

Sai dai duk da haka ana ci gaba da samun kashe-kashen al’umma da garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.

Leave a Reply