Tsohuwar Fursuna da ta kafa ‘yan sandan mata a Palastin, ta rasu

Fatima Barnawi, wadda mahaifinta ɗan Najeriya ne daga Borno (inda ta samu sunan Barnawi) kuma mahaifiyarta Bafalastiniya ce ‘yar ƙasar Jordan, ta kasance tana jagorantar tawagar ‘yan sanda a Gaza.

Fatima Barnawi, tsohuwar ‘yar sandan Falastinu, kuma mace ta farko da ta kasance fursuna a gidan yarin Isra’ila, ta rasu tana da shekaru 83 a ranar Alhamis a wani asibiti da ke birnin Alkahira na ƙasar Masar.

An haifi Barnawi a shekara ta 1939 a tsohon birnin ƙudus a ƙarƙashin ikon Burtaniya.
Ta girma a cikin al’ummar iyalai daga yankin kudu da hamadar sahara da suka zo birnin Ƙudus don aikin hajji ko kasuwanci kuma suka zauna a birnin.

Mahaifin Barnawi ɗan Najeriya ne, mahaifiyarta Bafalastsiniya ce. Bayan Nakba a 1948, ta ƙaura zuwa Jordan tare da iyayenta da ƴan uwanta biyar na ƴan shekaru, kafin ta koma Urushalima.

Ta kasance ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar Fatah na farko, ƙungiyar fafutukar neman wa Falastinawa ‘yanci a Yammacin Kogin Jordan, ƙarƙashin mulkin Jordan.

A watan Oktoban 1967, Barnawi ta zama mace ta farko da sojojin Isra’ila suka kama. Ta shafe kusan shekaru 11 a gidan yari saboda fafutukar da ta yi na yaƙi da mamayar da sojoji suka yi a gabashin Kudus, Yammacin Kogin Jordan da zirin Gaza, wanda ya fara a watan Yuni.

Wata kotun soji ta Isra’ila ta yanke mata hukuncin ɗaurin rai da rai saboda ta dasa bama bamai a sinimar Sihiyona da ke yammacin birnin Kudus, wanda sojojin Isra’ila ke yawan zuwa. Wani mai gadi na Isra’ila ne ya gano buhun bama-bamai mintuna kafin su tashi. An kuma kama ‘yar uwarta da wani ɗan ƙungiyar Fatah tare da yi musu shari’a dangane da harin, amma daga baya aka sake su.

KU KUMA KARANTA:Fatima al-Fihri: Macen da ta kafa Jami’ar farko ta Duniya, da kuma Laburare

Jam’iyyar Fatah mai mulkin Falastinu ta bayyana Barnawi a matsayin babbar mayaƙiya.

Ta shiga cikin yaƙin juya halin Falastinu tun a farkon matakin, kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa ƙungiyoyin fafutuka na ƙungiyar Fatah a cikin yankunan da aka mamaye,” in ji kungiyar.

A shekarar 1977 ne aka tasa ƙeyar Barnawi zuwa kasar Labanon, inda ta shiga ƙungiyar Fatah a matsayin ma’aikaciyar jinya, sannan kuma ta zama ma’aikaciyar kungiyar, wanda hakan ya sanya ta ƙulla alaka ta kut-da-kut da Yasser Arafat, shugaban kungiyar ‘yantar da Falastinu (PLO).

A shekarar 1985, Barnawi ta auri Fawzi al-Nimr, wanda ya kafa kuma jagoran ƙungiyar Akka 778, wanda ya ƙaddamar da hare-hare a cikin Isra’ila. An yanke wa Nimr hukuncin daurin shekaru 710 a gidan yari a shekara ta 1969 amma an sake shi a wata yarjejeniyar musayar fursunoni da Isra’ila a shekarar 1983. Ya kuma rasu a bara.

Bayan sanya hannu kan yarjejeniyar Oslo tsakanin PLO da Isra’ila a shekara ta 1993, Barnawi ta dawo tare da PA zuwa zirin Gaza kuma Arafat ya bata alhakin kafa ‘yan sandan Falasdinu mata, inda Barnawi ta zama Kanal, kuma ta jagoranci mata talatin.

Zuwa watan Yulin 2022, rundunar ‘yan sandan mata baki ɗaya tana da jami’anta 532. Shugaban Falastinawa Mahmoud Abbas ya ba Barnawi lambar yabo ta tauraruwar soja a shekarar 2015.

“Barnawi zata ci gaba da kasancewa abar tarihi mai haske a tarihin gwagwarmayar Falastinawa,” in ji Fatah a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Shugabannin Kungiyar da ‘yan kungiyar za su ci gaba da fafutukarsu har sai an samu nasarar ‘yancin ƙasa da Barnawi ta yi yaƙi, wanda ta wakilta ta kafa ‘yantacciyar ƙasar Falastinu mai cin gashin kanta tare da Kudus a matsayin babban birninta.”

Ƙungiyar fursunonin Falasdinu ta ce “ta rasa abin koyi na ƙasa wanda ta bar muhimman abubuwan tarihi na ƙasa da kuma ba da gudummawa ga gwagwarmayar Falastinawa shekaru da yawa”.

Har ila yau Barnawi ta kasance mamba a majalisar juyin juya hali ta Fatah, da majalisar koli ta soji ta juyin juya halin Palasdinu, da majalisar ƙasa ta Falasdinu da kuma babbar ƙungiyar matan Palasdinawa.

Ta gama karatu a matsayin ma’aikaciyar jinya a shekarar 1956 kuma ta yi tafiya aiki a wani asibiti a Saudiyya na tsawon shekaru biyu, inda ta koma gabar yammacin kogin Jordan a shekarun 1960.

A cikin hirarta ta karshe da ta yi da jaridar Albawaba ta Masar a watan Yuli, Barnawi ta bayyana zamanta a gidan yarin Isra’ila, inda ta girma a birnin Kudus, sannan kuma ta yi aiki da kungiyar Fatah a Lebanon, Tunisia da zirin Gaza. “Inata tunawa da abubuwa da yawa, da rayuwa ta data wuce kamar jiya, ban taɓa yin nadamar abin da na yi ba, kuma idan da za a ƙara bani damar lokaci, da na yi fiye da abinda na yi a baya,” in ji ta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *