Tashin Mu Ba Shi Ne Mafita Ba Domin Mutanen Mu Ma Basu Tsira Ba – Al’ummar Katari, Rijana Da Akilbu Sun Koka

0
297

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SABANIN labaran da ake ta yada wa marasa tushe daga majiyoyi masu alamar tambaya ciki har da wasu Kafafen yada labarai, al’umma mazauna yankin Katari, Rijana da Akilbu, sun koka da cewa al’ummomin su da dama sun kasance a cikin tashin hankali da tsoro, na cin zarafin da yan Bindiga, ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane suke musu akoyaushe.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a cibiyar kungiyar Yan Jaridu ta Najeriya, (NUJ) reshen Jihar Kaduna, Shugaban al’ummar Katari Danjuma Makeri wanda ya Jagoranci tawagar ta al’ummomin yankunan uku izuwa sakatariyar NUJ Kaduna, ya bayyana cewa yan Bindigan sun sha kashe mutanensu, yin garkuwa da su, tare da yi wa yaransu mata fyade wanda hakan ke daga musu hankula matuka.

Da suke bayani a madadin sauran al’ummar yankunan Bayanai sun yi yawa na nuna cewa, an yi garkuwa da mutanenmu, ko fyade, ko nakasasu ko kuma kashe su daga hannun wadannan ‘yan bindiga ko ‘yan ta’adda.

Ya kara da cewa wani abin mamaki shi ne, da yawa daga cikin manoman su ba sa iya shiga gonakinsu a kwanakin nan yayin da wasu kuma sai sun biya haraji ga ‘yan Bindigan kafin su shiga gonakinsu.

Ya ce “a yanzu haka Hakimin kauyen Rijana (Mista Ayuba Dodo Dakolo) da wasu al’ummarsa kusan 24 na hannun ‘yan Bindigan masu garkuwa da mutane. Hakazalika, mutane goma sha biyu (12) na al’ummar Katari ciki har da mata da yara suma suna hannun ‘yan Bindigan.

“A cikin watan Afrilun wannan shekara (2022), wasu ‘yan bindiga sun kashe tsohon sakataren reshen Akilbu, Mista James Abu a gonarsa. Hakazalika, an yi garkuwa da Martina John daga kauyen Katari, inda aka yi mata kisan gilla tare da jefa gawarta a kusa da Sabon Gayan a karamar hukumar Chukun ta jihar Kaduna.”

“Laifukan irin wannan kisan na gilla ga ƴan asalin ƙasar sun yi yawa a cikin al’ummomin mu wanda dukkan ‘yan bindigar ne suka aikata.” Ya ce

Shugaban ya ci gaba da cewa, Kamata ya yi a samar da ingantacciyar alaka tsakanin hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki a cikin al’ummomi don samar da hadin kai mai nagarta a yayin yakin da ake yi da ‘yan Bindiga a yankin.

Ya kara da cewa duk wuraren da za a iya gane inda ‘yan Bindigar ke amfani da damar da ba su dace ba don aikata munanan ayyukansu, ya kamata a sanya su ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro. Misali hanyar da ta ratsa babbar hanya tsakanin Katari da K/Kare, ya kamata a toshe ta ta hanyar kafa wani kakkarfan shingen sojoji a wurin.

“Tabbas, akwai wadataccen fili a cikin dajin gwamnati da ke tsakanin Katari, Gidan Busa, Akilbu da Rishi don ɗaukar duk wani katafaren tsaro ko kayan aiki.

“Ya kamata gwamnati ta tantance tare da bin diddigin duk rahotannin tsaro da suka shafi al’ummominmu don tabbatar da cewa ba aikin zato ba ne ko kuma tunanin wasu mutane da aka tsara don faranta wa wasu sha’awa.

“A tabbatar cewa jami’an tsaro da aka tura yankin sun yi aiki daidai da lissafin muhimman ayyukansu, kana a samar da Ingantattun kayan aiki tare da zaburar da duk jami’an tsaro da aka tura a cikin al’ummominmu. Ya kamata a inganta sashin binciken gine-ginen tsaro a yankin don fuskantar kalubalen lokacin.

“Daukar matasan mu cikin jami’an tsaro don ƙarfafa manufar aikin ‘yan sanda ta hanyar samun amincewar al’umma, tare da haɓaka matsayin ilimi na al’ummomi.

Duk wani dan al’ummarmu da aka gano a matsayin mai hada baki da ‘yan Bindiga, a yi maganinsa kamar yadda doka ta tanada. Ma’ana babu wanda zai tsira a cikin al’ummarmu idan aka same shi yana da hannu a cikin matsalar tsaro da gwamnati ke fuskanta.”

“Yi tanadin wani sashin ‘yan sanda don ɗaukar shari’o’in daga karamar hukumar Chikun a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, kana da tabbatar cewa jami’an tsaro da aka tura a cikin al’ummominmu suna aiki tare da masu ruwa da tsaki.”

“A takaice dai, ya kamata a bi diddigin bincike da gurfanar da su a gaban kotu ta hanyar amfani da hanyoyin da suka dace kuma a gwada su na lokaci maimakon a yi amfani da karfin tuwo bisa ga tsayuwar daka kamar yadda aka yi misali da shirin tashin al’ummarmu daga tushen kakanninsu tun a zamanin da.

Jagoran Al’ummomin ya bayyana cewa a wani bayani, Gwamnan jihar Kaduna ta fito karara ta yarda cewa ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar jihar Kaduna musamman babbar hanyar Abuja da kuma yankin Birnin Gwari wasu ’yan Boko Haram ne da Ansaru da suka zo su ke kokarin kafa sansani a jihohin Neja da Kaduna saboda suna la’akari da irin dazuzzukan Jihohin Kaduna da Neja sun dace da ayyukansu.

“Amma abin baƙin ciki a cikin a nan shi ne Gwamnan yana danganta ta’addanci ‘yan Bindigar da manoma masu rauni har ma da barazanar ko dai su ƙaura ko kuma ya kawar da su gaba ɗaya.”

“Abin tambaya a nan shi ne, ina hujjar da ke da alaka da wadannan ‘yan kasar masu rauni da ‘yan Bindigar dake kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna? To, me ya sa al’ummomi irin su Birnin Gwari, M/Jos, da suka shahara wajen aikata laifuka, ba a mayar da su cikin daji masu nisa ba? Me yasa kauyukan Adara kawai?”

Danjuma Makeri ya ce “akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa wasu masu hannu da shuni sun kuduri aniyar cin zarafin al’ummarmu ta hanyar amfani da duk wata dama da suke da ita kamar yadda ake iya gani a kasa.”

“Misali, a shekarar 2019, an samu wani lamari da aka gudanar da shi inda wasu jami’an tsaro daga rundunar sojojin saman Najeriya suka bayyana cewa sun tarwatsa gungun masu garkuwa da mutane da ake zargin suna yin garkuwa da su a cikin al’ummar Katari.

“Amma a cikin wannan kage da aka yi, wasu matasan mu da ba a san ko su wanene ba ne jami’an rundunar sojin sama suka tara su a filin wasa na GSS Katari da sunan gudanar da wani atisaye na izgili a lokacin.

“To wani abin mamaki da yammacin wannan rana, kafafen yada labarai sun fitar da wani rahoton da ke cewa wani Air Commodare Ibikunle Daramola (Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin saman Najeriya) ya yi nasarar kama wasu gaggan ‘yan bindiga a kauyen Katari da ake kyautata zaton yan ta’adda ne wanda aka gano masu laifi ne a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja yayin wani atisayen kwaikwayo na yau da kullun.

Game da harin da ‘yan ta’adda suka kai kan wani jirgin kasan fasinja da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna wanda ya afku a wani wuri kusa da kauyen Dutse kusa da gonakin Olam da ke cikin harabar garin Kaduna, kafafen yada labarai da dama na cikin gida da na waje ne suka karkatar da labarin da gangan don nuna cewa lamarin ya faru ne a tsakanin Kauyukan Katari da Rijana.

“A hakikanin gaskiya, akwai wasu lokuta da dama da kafafen yada labarai suka rika yada labaran ta’addanci dake faruwa kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna sau da yawa da ba a ambata a nan ba cikin wannan sakon namu ba wanda a inda aka sanya al’ummarmu da gangan ko dai bisa ga jahilci ko kuma wata muguwar manufa.” Ya Kalubalaci Kafafen yada labarai

Shugaban Danjuma Makeri ya Jaddada cewa sune kadai al’ummar da a duk fadin Jihar, ba a taba samun su da neman tashin hankali na kabilanci ko addini ba saboda tsananin zaman lafiyar dake tsakanin al’ummomin su duk da kasancewar akwai yarurruka da kabiloli daban-daban a cikinsu.

A karshe, al’ummomin sun shawarci Gwamnatin Jihar Kaduna da ta sauya ra’ayin na cewa za ta tashe su ko kawar da su ta karfi da yaji domin yin hakan ba shi ne mafita ga al’ummar kasar ba face neman hanya yin amfani da hanyoyin da suke dace tare hadin kan al’ummomin yankunan baki daya.

Leave a Reply