A Shirye Mu Ke Don Karbar Tubabbun Yan Boko Haram Da Za A Kawo Su Cikin Mu – Hardon Malkohi

0
273

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu.

A KOKARIN da su ke yi don amincewa da tubabbun yan Boko Haram da suka mika wuya wajen watsi da mummunar akidar nan ta ta’addanci, al’ummar garin Malkohi da ke karamar hukumar Yola ta kudu a Jihar Adamawa sun bayyana cewar, a shirye suke don karbar tubabbun ‘ya’yan Kungiyar ta Boko Haram da suka mika wuya don son komawa cikin al’umma.

Bayanin tabbatar da wannan abu dai ya fito ne daga bakin Hardon garin na Malkohi wadda sakataren sa Alhaji Bashir Aliyu ya wakilta yayin da jami’an hukumar nan ta kula da hakkin Dan Adam (NHRC) karkashin babban jami’inta Hillary Ogbonna da kuma jami’ar kula da harkokin yada labarai a hukumar Hajiya Fatima Agwai Mohammed tare da tawagar manema labaran da suke karbar horo kan gudummawar da za su iya bayarwa dangane da wayar da kan al’umma kan yafiya da Adalci ga al’ummar da ke da alaka da matsalar Boko Haram suka ziyarci garin na Malkohi don ganewa idon su irin halin da ‘yan Gudin Hijirar da ke Sansanin Malkohin ke ciki.

Hardon na Malkohi ya ci gaba da cewar, su mazauna wannan gari a Kullum a shirye su ke don ganin sun amince da karbar duk wasu tubabbun’ yan kungiyar ta Boko Haram da za a kawo gare su don zaunawa da su matukar hukumomin da abin ya shafa sun tantance su.

Ya kara da cewar a halin da ake ciki  shekaru uku da suka gabata an kawo musu wasu tubabbun na Boko Haram su kimanin 6 hade da iyalen su da aka tantance daga Gombe wadanda a yanzu suke tare da su.

Da jami’ar hukumar ta NHRC Fatima Agwai ke tambayar sa a kan ko daga lokacin da suka karbi wadannan tubabbun ko akwai wata matsala da suka fuskanta tare da su? Sai ya amsa da cewar lalle har kawowa ya yau ba mu taba fuskanta matsala ba tare da su, muna zaune lafiya da su, don har gonakin noma da wuraren sana’a muka ba su kuma ya zama wajibi da mu zama masu yafiya domin ta hanyar yafiya zamu samu zaman lafiya mai inganci. 

Tun farko da ta ke bayyana manufar zuwan su. babbar jami’ar yada labarai ta Hukumar ta NHRC Fatima Agwai ta bayyana wa Hardon na Malkohi cewar, sun kawo ziyarar ne don saduwa da su da kuma ‘yan Gudin hijirar da ke tare da su don jin irin damuwar su kana su kuma neme su da su zama masu yafiya da Adalci a tsakanin juna.

Shi ma da ya ke jawabi shugaban Sansanin ‘ yan Gudin Hijira na garin Malkohi Malam Umar Abubakar cewa, ya yi sun dade cikin wannan sansani kuma sun zo ne daga garin Gwoza akysarin su  sakamakon matsalar Boko Haram da suka tarwatsa su. 

Ya kara da cewa a yanzu haka sun dade a wannan sansani na Malkohi wanda a baya suna da ‘yan Hijira sama da dubu biyar amma sannu a hankali sama da dubu 3500 sun koma yankin su na Gwoza sakamakon zaman lafiya da ya fara wanzuwa. 

Ya kuma ce suna da koke ga gwamnati cewar da ta taimaka musu da abubuwan more rayuwa musamman abinci da sauran su kasancewar a halin yanzu suna fama da karancin abincin. 

Wakilin mu ya samu ganawa da daya daga cikin tubabbun Boko Haram din da ke sansanin na Malkohi mai suna Adamu Usman da aka ki amincewa da daukar hotonsa saboda matakan tsaro, ya bayyana cewar, shi yanzu sai godiya ga Allah SWT da ya kaddara ya tuba ya dawo cikin jama’ar sa, kuma yana godewa jama’ar sa da suka karbe shi tare da yafe masa abubuwan da suka faru a baya. 

Malam Adamu Usman ya kuma yi kira ga sauran ‘yan Uwansa da har yanzu suna cikin kungiyar ta Boko Haram da su watsar da wannan muguwar akida su dawo su mika wuya tare da watsar da malaman su kar su ji tsoron komai su taho za a karbe su ba za a musu komai ba. 

Daga nan sai hukumar ta NHRC ta mika kayayyakin tallafin da ta kaiwa ‘yan gudun Hijirar (IDPs) da suka hada da kwalayen Indomie da taliya da Makamantan su. 

Leave a Reply