Tarayyar turai za ta maye gurbin siyan gas daga Rasha zuwa Najeriya

0
155

Najeriya za ta zama ƙasa me samar da iskar gas ga ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙin Rasha da Ukraine, wanda da aka fara a ƙarshen watan Fabrairu.

Tawagar EU a Najeriya da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS, ne suka bayyana hakan a ƙarshen mako.

Mataimakin Darakta-Janar, Sashen Kula da Makamashi, Hukumar Tarayyar Turai, Matthew Baldwin ya yi wa manema labarai ƙarin haske a Abuja.

Baldwin ya je Najeriya ne domin ganawa da jami’an gwamnati da ‘yan wasa masu zaman kansu, ciki har da masu ruwa da tsaki a fannin makamashi.

Leave a Reply