Sojoji sun kuɓutar da uwa tare da ‘ya’yanta, da wasu mutum biyu a Kaduna

1
815

Dakarun ‘Operation Forest Sanity’ sun ceto wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su, wanda suka haɗa da uwa, da ‘ya’yanta a wani sintiri da suke yi a ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun na jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, ya ce sojojin sun fuskanci harin ne daga ‘yan bindiga a lokacin da suke sintiri a kan titin Birnin Gwari, Gayam, Kuriga, da Manini. Sojojin sun mayar da martani inda nan take suka fatattaki ‘yan ta’addan, wanda suka tsere zuwa cikin dazuzzuka, suka bar waɗanda suka yi garkuwa da su a hannun Sojojin.

Daga nan ne sojojin suka kuɓutar da mutanen bakwai da lamarin ya rutsa da su, waɗanda aka bayyana sunayensu kamar haka: Joseph Ishaku, John Bulus, Gloria Shedrack da ‘ya’yanta hudu; Jimre Shedrack, Jonathan Shedrack, Angelina Shedrack, da Abigail Shedrack.

Gwamnatin jihar Kaduna ta yabawa sojojin tare da gode musu bisa jajircewar da suka yi wajen ceto waɗanda lamarin ya shafa. Mutanen bakwai da abin ya shafa an sallamesu sun koma ga iyalansu.

1 COMMENT

Leave a Reply