Shugabancin Jama’a Na Da Matukar Wahala – Alhaji Hashimu Ibrahim

0
270

Daga; Musa Muhd Kutama, Kalaba.

SABON shugaban kungiyar al’ummar Arewa maso Yamma dake kudancin Kasar Najeriya Alhaji Hashimu Ibrahim ya bayyana Jagorancin al’umma da suka fito daga Jihohin Arewa maso Yamma aiki ne wurjanjan mai matukar wahala da neman addu’a Allah ya yi jagora.

Alhaji Ibrahim ya fadi hakan ne a garin Kalaba Jim kadan da tabbatar masa da mukamin shugaban kungiyar al’ummar sakkwatawa, Kabawa, zamfarawa da sauran Jihohin Katsina, kano, Kaduna da Jigawa wanda Mai martabar sarkin Hausasa-fulani mazauna Jihar kuros riba Alhaji Salisu Abba Lawan ya nada shi.

Sabon shugaban Alhaji Hashimu shi ne mutum na uku da aka nada kan wannan mukamin bayan wadanda suka shugabanci kungiyar.

Da yake zantawa da wakilin mu Jim kadan da nada shi mukamin, Alhaji Hashimu Ibrahim ya nuna matukar farin cikin sa da Kuma godewa Allah.

Ya ce “Ina mai matukar yin godiya ga Allah da kuma mai girma sarkin Hausawa-Fulani na kuros riba Alhaji Salisu Abba Lawan bisa duba cancanta da ya yi ya nada ni ya bani wannan mukamin.”

Ya ci gaba da cewa, cikin sakkwatawan da suka rike irin wannan mukami, akwai Alhaji Isah da kuma Alhaji Garba Dan bakyasuwa Zugana Sai kuma shi.

Shugaban Yan Arewa maso Yamma ya kara da cewa mai girma sarkin Hausawan ya duba a tsakanin mutum biyu wa yafi cancanta da a nada shi mukamin shi ne ya zabe shi aka bashi.

Alhaji Ibrahim shugaban Al’ummar na uku ya bayyana Hanyoyi da ya ce zai bi su idan ya bisu zai cimma nasarar hada kan jama’a ba tare da an samu wata baraka ko cikas ba.

“Za a zauna ne da Al’ummar ko wace Jiha Shi ma ya zauna da mutanen sa shi ne idan suka hada kan su shi ne sai suzo nan wurina mu zauna muha yadda zamu ci gaba da zama da yan uwan tare da sauran mutanen wadannan Jihohin tunda mu ne muke shugabanci.”

Karshe, ya sha alwashin da yardar Allah zai hada kan al”umomin da aka dora Masa alhakin shugabancin su a kansa an hada kai Alhaji Garba Gada da ta  daga cikin dattawan unguwar Hausawa ya ce babu abinda sabon shugaban ke bukata face addu’ar Allah ya yi masa jagora, Ya ba shi ikon cimma buri a nauyin al’umma da aka dora masa.

Leave a Reply