Har Yanzu Ba A Daina Kashe Mutanen Kataf Ba – Shugaban Al’ummar ATYAP

0
260

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A sakamakon matsalar yawan Kashe – kashen da yake addabar al’ummar yankin Kudancin Kaduna wanda ya-ki-ci ya-ki-cinyewa, al’ummar yankin Kataf sun koka bisa irin yadda al’amura suke kara tabarbarewa a yankin nasu dake Kudancin Jihar Kaduna.

Shugaban Kungiyar al’ummar ATYAP Mista Samuel T. Achie, a wani taron manema labarai da suka gudanar a cibiyar Kungiyar Yan Jaridu (NUJ), reshen Jihar Kaduna a ranar litinin, ya yi Allah-wa-dai da halin ko-in-kula wanda Gwamnatin Jihar ta yi duba da irin halin da suka tsinci kansu.

Ya kara da cewa tun a shekarun baya lokacin da su ka fara bayyana kokensu da nuna damuwa bisa irin halin da suke ciki, sun yi tsammani al’amura zasu canza ta fuskar samun cin nasara da samun sauki ta yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, toh amma har yanzu babu canji a cikin al’amarin.

Ya ce “a cikin mako guda, akalla an Kashe Mutanen Katab ashirin da biyu a yankin ATYAP, an kona gidaje arba’in da biyar, an mayar da mutane sama da dari uku yan gudun Hijira da suka koma zaman a shingen yan gudun Hijira.”

“Gwamnatin ba ta damu da halin da muke ciki ba wanda a kullum kara Kashe mana mutane ake, kuma musamman a duk lokutan da muka yi wani yunkurin zaman sulhu wanda ba ma kammala shi ba tare da mun samun wani mummunar labarin aukuwar wani al’amari haka ba.”

“Ya kamata Gwamnati ta sake duba lamarin aikin Jami’an tsaron dake yankin domin sanin ko ana samun nasara ko kuwa da akwai bukatar a canza salon saboda wani lokacin suna kallo ana kashe mutane a kusa dasu amma basa daukar wani kwakkwarar matakin da ya dace na ganin cewa ba a sake aikata wani makamancin irin laifin ba.”

“Mun dade muna samun zaman lafiya da al’ummar Hausawa da ke zaune a garin Zango, toh amma abin mamaki shi ne a duk lokacin da muka kora Fulanin dake mana ta’asa, su Hausawan garin ke basu mabuya don haka muna da bukatar a kori duk wani Fulanin dake Kasar Zango saboda muna zargin akwai hadin gwiwa a tsakaninsu da Hausawan.” Inji Shugaban Al’ummar ATYAP

Acewarsa, Gwamnatin Jihar ta bayyana cewa tana da kyakkyawar alaka tsakanin ta da masarautar ATYAP wanda hakan yasa ta ke girmamata, toh amma sai dai su al’ummar yankin Katab din ba su ga alamun haka din ba ta yadda aka mayar dasu saniyar ware ba tare da ana kai musu wani agaji a kan matsalar tsaron da suke fama da ita ba.

A karshe, Mista Samuel Achie ya buƙaci al’ummar yankin Kudancin Kaduna da su kara hakuri da kiyaye bin Dokoki da Oda a duk yanayin halin da suka tsinci kansu don neman canjin salo na samun zaman lafiya a yankin Kataf, Kudancin Kaduna da Jihar baki daya.

Leave a Reply