Shugaban Gidauniyar Tamallan Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Karamar Sallah

0
268

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SHUGABAN Gidauniyar Tamallan Dokta Saleh Musa Wailare ya taya al’ummar musulmi murnar Zagayowar Karamar Sallah tare da fatan za a ci gaba da yin aiki da abubuwa na alheri da aka koya cikin watan Ramadan.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mataimakinsa na musamman kan kafafen yada labarai Jabiru Hassan, Dokta Wailare ya bayyana watan Ramadan a matsayin wata da yake koyar da darussa masu tarin yawa wadanda kuma suke zamowa jagora ga al’ummar musulmi a duk inda suke.

Sannan ya nunar da cewa a cikin watan Ramadan an sami karin ilimi na kyautata zamantakewa da kusanta ga Allah da kuma taimakon marasa karfi wanda hakan babbar nasara ce ga wadanda suke da damar tallafawa al’uma musamman marayu da iyayen marayun.

Dokta Saleh Musa Wailare ya yi amfani da wannan dama wajen yin fatan alheri ga al’ummar kananan hukumomin Dambatta da Makoda da Jihar Kano dama daukacin musulmi duniya baki daya bisa kammala azumin watan Ramadan na bana cikin nasara.

Shugaban Gidauniyar Tamallan wanda kuma shine dan takarar wakilcin mazabar Dambatta da Makoda a majalisar wakilai ta tarayya, ya jaddada cewa yana wannan takara ne domin kawo managarcin ci gaba a wadannan kananan hukumomi ta yadda zamantakewa zata kara albarka.

Leave a Reply