Shugaban ƙungiyar ƙasashen Duniya masu haƙo man fetur ta Duniya ya rasu, bayan kawowa shugaba Buhari ziyara Jiya-Jiya

0
501

Allah yayima Muhammad Barkinɗo rasuwa cikin daren jiya talata, wajen misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare.

A yayin ziyarar da ya kaima Shugaba Buhari a jiya Talatar, Barkinɗo ya bayyana ma shugaban ƙasar cewa lokacin saukar shi daga Muƙamin shugaban wannan kungiyar ta ƙasashen Duniya masu hako Man Fetur ta Duniya yayi. Hakan yasa akayi murna tare da karrama shi.

Baya ga ziyarar Aso Rock, Mista Barkindo ya kuma gabatar da jawabi a ranar Talata a taron mai da iskar gas na Najeriya da ke gudana a Abuja.

Haƙika, mutuwar Barkinɗo babban rashi ne ga iyalansa, NNPC, kasar mu Najeriya, ƙungiyar OPEC da kuma ƙungiyar makamashi ta duniya.

Nan ba da jimawa ba za a sanar da shirye-shiryen jana’izar.

Leave a Reply