Sarkin Saudiyya ya bayar da hutu domin murnar nasarar kasar kan Argentina

0
260

Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya bayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar, bayan da Saudiyya ta lallasa Argentina da ci 2-1 a gasar cin kofin duniya ta Qatar 2022.

Saudi Gazzette ce ta sanar da hakan a shafin Twitter, a yammacin ranar yau. Ko da yake an yi hasashen Argentina ce za ta yi nasara, saboda tana tare da fitatcen ɗan wasan a duniya, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai, Lionel Messi, sun yi ta faman samun gindin zama a wasan inda suka rasa dukkan hari ukun da suka kai.

Sanarwar ta ce, “Sarki Salman ya ba da umarnin cewa gobe Laraba, za ta kasance hutu ga dukkan ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da kuma ɗalibai a kowane mataki na ilimi don murnar nasarar da #SaudiArabia ta samu kan Argentina a #Cup2022.”

A yanzu dai Saudiyya ta buga wasanni 17 a gasar cin kofin duniya ta FIFA, inda ta yi rashin nasara a wasanni 11 sannan ta yi kunnen doki a biyu. Sau ɗaya ne Saudiyya ta tsallake zuwa matakin rukuni a gasar cin kofin duniya a shekarar 1994.

Leave a Reply