SANARWA: Hasashen NIMET, NIHSA ya ja hankalin Jihar Yobe kan ambaliyar ruwa

3
332

Hukumomin kula da yanayi a Nijeriya: ‘Nigeria Meteorological Agency (NIMET)’ da takwararta ta ‘Hydrological Services Agency (NIHSA)’ sunyi hasashen cewa jihar Yobe ta na ɗaya daga cikin jihohi 32 a ƙasar nan wayanda ake tsammanin za su fuskanci ambaliyar ruwa a kwanaki uku masu zuwa.

Hukumomin sun bayyana hakanne a cikin wani sakamakon yanayi da suka fitar ranar Talata.

Sunyi hasashen cewa za’ayi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya wanda zai janyo ambaliya a jihohin a Yobe da jihohi kamar Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna, Kano, Jigawa da Bauchi.

Sauran sun hada da Gombe, Kebbi, Neja, Babban Birnin Tarayya na Abuja, Plateau, Adamawa, Taraba, Kwara, Oyo, Lagos, Ondo, da Ogun. Haka abin zai kasance a Edo, Delta, Bayelsa, Cross River, Akwa Ibom, Benue, Inugu, Ebonyi, Imo, Anambra, Abia da Rivers.

Hukumomin sun ja hankali da cewa ambaliyar zai iya shafar gidajen al’umma, gonaki, hanyoyi da gadoji.

Bayan wannan hasashe da hukumomin suka yi, yana da muhimmanci jama’a su dauki ingantaccen mataki, musamman al’ummar jihar Yobe dangane da sakamakon da zai biyo bayan ambaliyar ruwan, wanda ya zo ta dalilin sauyin yanayin da aka samu a wannan shekara.

Wanda sakamakon hakan, jama’ar da suka fi fuskantar matsalar ambaliyar ruwan sune qananan hukumomin Potiskum, Gashua, Nguru, Fika, Gaidam, Damagum, Gujba, Gulani, Damaturu haxi da garuruwan da ke zaune kusa da hanyoyin ruwa, gwamnatin jihar Yobe tana shawartar su cewa su dauki ingantattun matakai a irin wannan lokaci na damina.

A ƙoƙarin ganin ta ci gaba da kare rayuka da dukiyar jama’ar jihar, ta hanyar amfani da matakai daban-daban, gwamnatin jihar Yobe ta dauki muhimman matakai da ingantattun tsare-tsare wajen bayar da daukin gaggawa: yunqurin daqile afkuwar ambaliyar, shirin ko-ta-kwana, kai daukin gaggawa tare da na aikin farfado da wuraren da ibtila’in ya rutsa dasu, ta hanyar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Yobe (SEMA) da takwararta ta NEMA.”

Hukumar SEMA kowane lokaci a shirye take wajen aiki babu dare ba rana a duk lokacin da wani ibtila’i ya faru a fadin jihar, domin kai daukin gaggawa, tallafa wa wayanda abin ya rutsa dasu da sake farfado da wuraren da al’amarin ya shafa.

Dadin daɗawa gwamnatin jihar Yobe za ta dauki matakin kafa kwamitocin bayar da agajin gaggawa a qananan hukumomin jihar (LGEMC) wayanda za su rinqa bayar da tallafin gaggawa a matakin farko ga jama’a, kafin zuwan Hukumar SEMA.

Bayan ingantattun matakan da gwamnatin jihar ke dauka domin magance matsalar ambaliyar ruwan, ana kira ga jama’a da cewa su nisanci al’adar zuba shara kan hanya ko a magudanun ruwa, musamman unguwannin da suke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa, da bayar da kula ta musamman ga raunana; tsoffi, naqasassu da yara, a irin wannan lokaci.

Akwai buƙatar kwamitocin kula da tsabtace muhalli a qananan hukumomi har da qungiyoyin taimakon kai da kai, su fadakar da mambobin su wajen ci gaba a aikin tsabtace muhalli ta hanyar yashe magudanun ruwa da gyara hanyoyin ruwa da dakatar da jama’a yin gini kan hanyar ruwa.

Manoman mu, musamman fadama da wayanda gonakin su suke kusa da koguna, muna basu shawara su yi amfani da sauyin yanayin wajen samun zarafin shuka amfanin gonarsu zuwa girbi, ba tare da fuskantar wata barazana ga amfanin ko dabbobin su ba.

Yusuf Ali
Babban Mai Taimaka Wa Gwamna Mai Mala Buni a Fannin Yada Labaru na Zamani Tare Da Dabarun Sadarwa.

3 COMMENTS

Leave a Reply