Connect with us

Labari

Rashin Tsaro A Najeriya Yana Ci Gaba Da Tabarbarewa Duk Da Alkawuran Da Buhari Yake Dauka

Published

on

A Najeriya duk da alkawuran da shugaban kasar Muhammad Buhari ya sha nanatawa na hannunta kasa mai cikakken tsaro ga gwamnatin da za ta gade shi, har yanzu jama’a na ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci a yankuna daban daban.

A wannan mako ma mahara sun kai farmaki a Sokoto inda suka hallaka mutum hudu kuma suka jikkata wasu.

Lokaci na ta tafiya ga karewar wa’adin gwamnatin mai mulki a Najeriya kuma ga jama’a na ci gaba da fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga, ana samun salwantar rayuka da dukiyoyin jama’a musamman na mutanen arewa abinda kan iya haifar da ayar tambaya akan ko za’a samu cikar alkawullan shugaba Muhammad Buhari na hannun ta kasa mai cikakken tsaro ga gwamnatin da zai mikawa mulki.

A jihar Sakkwato ma dake arewa maso yammacin kasar a wannan karahen mako mahara sun afkawa kauyen sabon garin dole, dake karamar hukumar Goronyo har suka hallaka wasu mutane.

Wani mazaunin garin ya shaida wa muryar Amurka kan abinda ya faru inda ya ce sun far masu ne daddare kuma suka dinga harbin duk wadanda su ka yi karo da su da ba su ma san abun da ake ciki ba. Sun kashe mutane da dama, sun kuma raunata wasu wanda yanzu haka suna asibiti.

Duk yunkurin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Najeriya akan batun ya ci tura.

Amma shugaban karamar hukumar Goronyo Abdulwahab Yahaya Goronyo ya tabbatar da kai harin, sai dai saboda baya garin, yace ba zai ce komai ba sai ya je yaga abinda ya faru.

Kawo zuwa hada wannan rahoto an kira sa fiye daya bai karba kiran ba, kuma an tura masa sako a waya bai mayar da jawabi ba.

Mun kuma zanta da mai sharhi akan lamurran yau da kullum Farfesa Bello Badah ko yake suke kallon kai hare-hare ga jama’a musamman duba da alkawullan shugaba Buhari na samar da cikakken tsaro kafin karewar wa’adin gwamnatinsa, ya bayyana cewa shugaba Buhari yayi alkawarin bada tsaro, kuma ‘yan najeirya sun sa ido suna kan jira. Sha’anin tsaro sai da haddin kai kuma babu haddin kai saboda mutane basu da kwanciyar hankali, ga talauci, rashin aiki da tsadar mai.

Shugabannin kananan hukumomi sune shugabanni mafi kusa ga jama’a, sai dai wasu lokuta wasu sukan kauracewa yankunan su dawo cikin birane, su bar jama’a suna neman agaji har dai in mahara sun kutso yankunan su.

Yankin Goronyo dai yana a gabascin Sakkwato kuma ya taba fuskantar harin da ake ganin na ramuwar gayya ne daga ‘yan bindiga wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Matsalar rashin tsaro dai zuwa yanzu ta dauki rayuka da dama tare da daidaita yankuna da al’ummomi a arewacin Najeriya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labari

EMAS69 • LINK ALTERNATIF SPORTBOOK SBOBET

Published

on

By

Emas69 adalah bandar taruhan sportbook sbobet terlengkap yang saat ini sangat dikenal seluruh masyarakat Indonesia dengan melalui link alternatif Emas69. Pada permainan taruhan sportbook, setiap pertandingan sepak bola yang dilangsungkan dapat dijadikan sebagai tempat bagi seluruh masyarakat Indonesia untuk melakukan taruhan dengan menggunakan uang asli. permainan taruhan bola online dapat dilakukan dengan bebas sesuai dengan pertandingan yang berlangsung dan juga team sepak bola yang disenangi untuk memperoleh kemenangan dan kepuasan dari setiap taruhan sportbook di situs Emas69.

Continue Reading

Labari

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Published

on

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi - TUC/NLC

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

Gamayyar ƙungiyar ƙwadagon Najeriya ta ce tayin Naira 70,000 da shugaba Tinubu ya yi a matsayin mafi ƙarancin albashi da babu ne gara ba daɗi.

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

KU KUMA KARANTA:NLC ta ƙira taron gaggawa bayan gwamnati ta jingine batun ƙarin albashi

Wannan dai na nuna a karo na farko tun neman mafi ƙarancin albashi mafi yawa a Najeriya Naira 615,00 ya sauƙo Naira 477,000, shugabannin ƙwadagon sun maida wuƙa kube ta hanyar yin na’am da tayin da gwamnati ta yi.

Bayan kammala ganawa babban sakataren ƙungiyar ƙwadagon ta TUC Komared Nuhu Toro ya ce sun amshi tayin da gabatar da hakan gaban majalisun su “mun kai majalisar ƙolinmu, tayin da shugaban ƙasa ya bayar sun kuma lamunta da shi da fatan Allah ya sa albarka…ai Naira 70,000 ɗin nan da babu ne gara ba daɗi.

Tuni ma’aikata na sassa daban-daban suka fara maida martani da mafi sauƙin shi ne na nuna ba abun da suka iya don jagorori sun miƙa wuya.

Malamin makaranta Muhammad Bello Nawaila ya ce ba wani tasiri da mafi ƙarancin albashin zai yi in an duba ɗan karen tsadar rayuwa.

Ita ma ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyin arewa CNG da ke marawa gwagwarmayar ma’aikatan baya ta ce matuƙar shugaba Tinubu bai yi garambawul ga lamuran walwalar ma’aikata da matasa ba, za a iya fuskantar ƙalubale “mu na gujewa guguwar juyin juya hali a Najeriya matuƙar gwamnati ba ta farka ta ɗauki matakan gaskiya na zahiri ba.”

Alamu na nuna batun neman ƙarin mafi ƙarancin albashi zai dakata zuwa wani lokaci don ‘yan ƙwadagon sun yaɗa gora sai komawa kan batun tsadar rayuwa.

Continue Reading

Kasashen Waje

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Published

on

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump - Pennsylvania

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Sakataren tsaron cikin gida na Amurka, Alejandro N. Mayorkas ya fitar da wata sanarwa game da harbin da aka yi a wurin yaƙin neman zaɓen tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump a jihar Pennsylvania da safiyar yau.

A cikin sanarwar, Sakataren tsaron cikin gidan na Amurka Mayorkas ya bayyana cewa, “Ni da Daraktan ma’aikatar leƙen asiri Cheatle mun yi wa Shugaba Biden bayani game da harbin da aka yi yau a Pennsylvania. Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) da Ma’aikatar Leƙen Asiri suna aiki tare da abokan aikinmu, masu kula da kiyaye doka don gudanar da bincike kan harbin.

KU KUMA KARANTA:Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan takarar Donald Trump

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna Allah wadai da wannan tashin hankalin da kakkausar murya tare da yaba wa hukumar leƙen asiri bisa matakin gaggawar da ta ɗauka a yau. Muna tare da Shugaba Biden, tsohon Shugaba Trump, da yaƙin neman zaɓensu, kuma muna ɗaukar duk matakin da ya dace don tabbatar da tsaronsu. Kula da tsaron ’yan takarar Shugaban ƙasa da kuma taron yaƙin neman zaɓensu na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da sashenmu ke ba da fifik

Tun farko Mai magana da yawun ma’aikatar leƙen asiri Anthony Guglielmi ya fitar da sanarwa a dandalin sada zumunta X, cewa, “Ma’aikatar leken asiri ta aiwatar da matakan kariya kuma tsohon Shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya. Yanzu haka Hukumar tana gudanar da bincike, ta kuma sanar da Hukumar Binciken manyan laifuka ta FBI.”

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like