Ramadan; NUJ Kaduna Ta Buƙaci Al’ummar Musulmi Da Yin Addu’o’in Samun Zaman Lafiya

0
464

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A YAYIN da al’ummar musulmin kasar nan suka bi sahun sauran takwarorinsu na duniya wajen gudanar da mirnar zagayowar watan azumin Ramadan, Kungiyar Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, ta bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokacin wajen neman yardar Allah da kuma shigar da Ubangijinsu cikin lamura dawo da zaman lafiya da hadin kai da samun mafita a Jihar da kasar baki daya.

A wata sanarwa da sakataren Kungiyar, Gambo Santos Sanga ya fitar mai dauke da sa hannun shugabar hukumar, Asma’u yawo Halilu, ta bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan dama wajen yin nazari.

Sanarwar ta kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi addu’ar Allah Ya kawo wa Kasar dauki da kuma kariya tare da warkar da kasar nan daga kalubalen da take fuskanta na rashin tsaro.

Kungiyar NUJ, ta kuma bukaci al’ummar musulmi da wadanda ba musulmi ba da su kasance masu kaunar juna da zaman lafiya da juna domin ci gaban tattalin arziki da siyasa na kasar nan.

Ta kara da bayyana fatanta na cewa Jihar Kaduna da ma Najeriya za su tsira daga matsalolin da suka addabi al’ummar kasar bisa ga dukkan kalubalen da ke gabanta.

A karshe, Kungiyar ta NUJ Kaduna ta yi addu’ar fatan Allah ya karbi ibadun dukkan musulmi Yasa su yi Azumin Ramadan lafiya, kana Ya kuma kawo mana zaman lafiya a siyasar 2023.

Leave a Reply