Ramadan: Dokta Wailare Ya Yi Fatan Alheri Ga Al’ummar Muslumi

0
331

Daga; JABIRU A HASSAN, Kano.

DAN takarar majalisar wakilai ta Tarayyar Najeriya daga mazabar Dambatta da Makoda Dokta Saleh Musa Wailare ya mika sakon fatan alheri ga al’ummar wannan mazaba dangane da zagayowar watan Ramadan mai albarka.

Sannan ya yi fatan alheri ga daukacin musulmin Jihar kano da Najeriya da kuma na duniya baki daya, tare da fatan Allah Yasa a kammala wannan ibada cikin nasara.

Bugu da Kari, Dokta Saleh Musa Wailare ya yi kira game Al’ummar musulmi su ci gaba da addu’ar samun dawwamammen Zaman lafiya da karuwar arziki ta yadda zamantakewa za ta kasance mai kyau.

Sannan ya sanar da cewa tafiyar siyasa tsakaninsa da al’umomin Dambatta da Makoda tana nan daram kuma zai ci gaba da kokarin kyautata wannan dangantaka ta kowace fuska.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here