PDP-NYA Ta Taya Ashiru Kudan Murnar Lashe Zaben Fidda Gwani, Ta Jinjinawa Jam’iyyar Ta PDP

0
396

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WATA kungiyar matasa ta Jam’iyyar PDP wato People’s Democratic Party National Youth Agenda, (PDP-NYA) reshen Jihar Kaduna, ta taya Rt. Hon. Isah Ashiru Kudan murna lashe Zaben fidda gwani a yayin da ya zama dan takarar gwamna da ke rike da tikitin jam’iyyar a jihar, ta kuma yabawa jam’iyyar bisa gudanar da zaben fidda gwani na gaskiya da lumana a jihar.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar (PDP-NYA) na Jihar, Kwamared Ahmad Ashir ya sanya wa hannu, ya bayyana jin dadinsa bisa nasarar da dan takarar ya yi tare wakilan jam’iyyar bisa kokarin ganin an samu dan takarar jam’iyyar da zai yi zarra a zaben duka gari mai zuwa na shekarar 2023.

Kwamared Ashir ya kara da cewa, zabin da ke gabansu a zaben fidda gwani na 2022 shi ne tsakanin shugabanni nagari da miyagu, kuma tsakanin wakilcin da ya dace na al’umma da kuma na bata suna. Tsakanin shugabannin da za su kasance tare da jama’a tun daga farko bayan sun ci zabe har zuwa karshen wa’adinsu da kuma Shugabannin da za su yi watsi da jama’a bayan sun cimma burinsu amma daga baya su fara tuntubar mutane idan lokacin wani zabe ya yi.

Ya ce, “zabe ne tsakanin shugabanni ne da suka wawure mana biliyoyin Naira na ayyukan mazabunmu da kuma shugabannin da ke da muradin sauya rayuwar Talakawa gobe.

“Na biyu, zabe ne tsakanin shugabanni da za su rika bin al’adar ba mu abinci su sayi kuri’unmu da kuma shugaban da ke da muradin tallafawa kan yadda za mu sayi kayan abincin kanmu a rayuwarmu, zabe ne tsakanin shugabannin da ba ruwansu game da mutanensu da ake kashewa da shugabannin da suka shirya don kare jama’a.

“Zabe ne tsakanin shugabannin da suke ganin siyasa wata dama ce ta yin hidima don amfanin kowa da kuma shugaban da yake kallon siyasa a matsayin kasuwanci ne suke wawure duk wasu kudaden da ake son ci gaba. To, sai yaushe za mu kasance cikin talauci da dukiyar mu?” Ya tambaya

“Wakilan Jam’iyya, shugabanni da masu ruwa da tsaki a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna, kun zaba mana zabin mu mai girma Sarkin Bai Zazzau Honarabul Isah Ashiru Kudan wanda zai gyara rayuwar kowa a yau da gobe idan Allah ya kaimu a Jihar Kaduna.

“Kun sauke nauyin da ya rataya a wuyanku a jihar ku ta hanyar yanke wannan shawara mai kyau na zaben shugaban da ke shirye ya yiwa talakawa aiki, mutum mai tausayin dan Adam da kwarjinin shugabanci.

“Saboda haka, ina kira ga wadanda suka yi nasara kuma da wadanda suka fadi zaben fidda gwani tun daga majalisun Jihohi da na Wakilai da na Sanata da kuma na Gwamna da su dauki kansu a matsayin iyali daya mu hada kai domin samun nasarar hadin kan Jam’iyyarmu da kuma Jihar musamman domin tabbatar da cewa Jihar mu ta dawo daga fagen mulkin mallaka rashin shugabanci nagari” Inji Kwamared Ashir.

Ya kara da nanata cewa (PDP-NYA), Kungiya ce da ke aiki a kowane mataki na ci gaban jam’iyyar da kuma matasa baki daya ta hanyoyin dabarun ci gaban jama’a da wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaben jam’iyyar kamar yadda suke da karfin jefa kuri’a.

A karshe Shugaban na Jiha, ya bayyana cewa za su ci gaba da bayar da goyon bayansu, tattaunawa da kuma zaburar da masu kada kuri’a ga daukacin ‘yan takarar jam’iyyar PDP tare da goyon bayan jam’iyyar PDP ta Kaduna da kuma fatan karbar madafun iko a 2023.

Leave a Reply