NLC Kaduna, Ta Yi Allah-Wadai Da Sabbin Hare-Hare Da Kashe Mutane A Garin Kagoro

0
284

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR kwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kaduna, ta yi Allah-wadai da sabbin hare-hare da kashe-kashen mutane da barnata dukiya a garin Kagoro da ke karamar hukumar Kaura a Jihar Kaduna da kewaye.

Shugaban Kungiyar, Kwamared Ayuba Magaji Suleiman ne ya yi Allah-wadai da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kaduna.

Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya yi kira ga gwamnati da Jami’an tsaro da su tabbatar da sun binciko tare da hukunta masu aikata irin wadannan miyagun ayyukan don sun fuskanci hukumci.

Ya tunatar da al’ummar Kudancin Kaduna cewa babu wani ci gaba mai ma’ana da za a samu idan an samun irin wadannan rikice-rikicen.

Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya shawarci gwamnati a kowane mataki da ta tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada.

Ya kuma yi kira ga wadanda abin ya shafa da kada su dauki doka a hannunsu, su bar jami’an tsaro su kammala bincikensu.

A karshe, Kungiyar ta jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu yayin rikicin tare da yin addu’ar Allah ya kawo dauki.

Leave a Reply