Ni Ne Wannan Dan Najeriyan Da Ya Kasance Na Kowa Ne A Ko’ina – Sanata Anyim

0
381

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON shugaban majalisar dattawa, Senata Anyim Pius Anyim ya bayyana matsalolin Najeriya a matsayin masu sarkakiya da ke bukatar shugabancin da ya dace ya tunkare su domin kawo Karshen matsalolin da ake fuskanta.

Ayim ya yi wannan magana ne a ranar Litinin yayin da yake jawabi ga wakilan Jam’iyyar PDP a sakatariyar jam’iyyar da ke Kaduna.

Ya kara da cewa matsalolin da ake fuskanta na da bukatar wani jajirtaccen mutum kamar shi domin kowa Karshen abubuwan da ake fuskanta, domin acewar wannan wani abu ne daya taba yi a lokacin da yake rike da shugabancin Majalisar Dattawa a matsayin Shugaba.

Ya ce “ni ne wannan dan Najeriyan da tun da nake a rayuwata ban taba tafiya na bar kasar nan sama da sati biyu, kuma yara na a kasar nan suke karatu kuma wannan dan Najeriyan da ya kasance na kowa ne a ko’ina.”

“Idan muna da shugabanci nagari, komai zai yi daidai, kuma ni ne wannan Shugaban wanda Kasar Najeriya nan ta ke bukata, kuma idan kuka tura ni a wannan aiken, zan dawo muku da irin kyakkyawar tsohuwar rayuwar da kuka saba da ita ada.”

“Yau a Najeriya mutane da yawa za su fito su ware rashin tsaro, wasu kuma za su ware tattalin arziki, amma zan iya fada muku cewa matsalolinmu suna da sarkakiya, wani kuma yana haifar da wani.

“Idan ka tambaye ni, kalubalen da ke gabanmu a yanzu shi ne samun ingantaccen shugabanci wanda ya san matsalolin da yadda za a gyara matsalolin,” Anyim ya bayyana.

Ya tuna cewa ya shafe shekaru 33 yana aikin gwamnati.

“Na kasance a kusa da gwamnati da shugaban kasa; Na yi aiki a matsayin Sanata; Na taba zama shugaban majalisar dattawa.

“A lokacin da aka fi fama da rikici a waccan majalisar dattijai lokacin da na zo, na sake haduwa da kowa kuma rikicin ya ragu,” inji shi.

Ayim ya ci gaba da cewa Najeriya na bukatar shugaba irinsa ya fito ta hanyar fahimtar juna da nufin magance kalubalen kowace kungiya ko bangaren kasar nan domin samun zaman lafiya.

“Aikina ne, na yi alƙawarin cewa idan kun ba ni dama, za mu yi aiki tare, mu mai da Najeriya yadda muke so ta zama.

“Mai gina kasa ne kadai zai iya karfafa kafuwar kasarmu, kuma an fara zabar mutumin da zai jagoranci Najeriya zuwa ga wadata da tsaro,” in ji Ayim.

A cikin sakon nasa na fatan alheri, Sen. Ahmad Makarfi ya bayyana Sanata Ayim a matsayin daya daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar jam’iyyar, tare da yi masa fatan samun nasara gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Sanata Anyim ya rike mukamin shugaban majalisar dattawa daga shekarar 2000 zuwa 2003, da kuma sakataren gwamnatin tarayya daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Leave a Reply