2023 Shekara Ce Da Za Mu Yanke Hukumcin Ko Najeriya Za Ta Yi Nasara Ko Akasin Haka – Hayatu-Deen

0
374

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WANI dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Mohammed Hayatu-Deen, ya bukaci wakilai da kada su kasance masu tada hankali, amma su kasance masu hankali yayin kada kuri’unsu a zaben fidda gwani, domin samun damar neman hada kan yan Najeriya da ci gaban Kasar.

Hayatu-Deen ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar na Jihar Kaduna a sakatariyar jam’iyyar da ke Kaduna, Inda bayyana cewa shekarar 2023, lokaci ne da yan Najeriya zasu yanke hukunci a kan ko Kasar za ta yi nasarar ci gaba da kasa ko akasin hakan.

Ya kara da cewa wakilai zasu taka rawar gani wajen tantance zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, inda ya kara da cewa, “Ina rokon ku da kada ku kasance masu tunani ko jin dadi amma ku kasance masu hankali wajen gudanar da ayyukanku.

Hayatu-Deen ya kuma yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su guji duk wani nau’i na banbance-banbance tare da zabar ’yan takara masu sahihanci da za su kai Najeriya ga gaci.

Ya ce “tun da nake a rayuwa lokacin da nake yaro, ban taba ganin wani lokacin da abubuwa suka runchabe ba na zubar da jini na ba-gaira ba-dalili irin yanzu, don haka yanzu lokaci ne da kasar mu ya kamata ta samu canjin shugabanci nagari daga wajen wani.”

“Ni mutum ne lafiyayye, ni mutum ne mai kwarewa, ni mutum ne mai kokari wanda aka da shaidar zaman shi na kwarai, don haka nake bukatar ku zabe ni a matsayin dan takarar da zaku tsayar a zaben fidda gwani na wannan Jam’iyyar ta PDP don zama Shugaban Kasa a zaben duka gari.

Dan takarar, ya yi nadama kan illar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da aka shaida a kasar. Sai dai ya ba da tabbacin cewa idan aka ba shi dama ya jagoranci kasar, zai fito da dimbin gogewar da yake da shi domin kyautata rayuwar talakawa.

Sanata Ahmad Makarfi a cikin sakon fatan alheri a wurin taron, ya bayyana Hayatu-Deen a matsayin mai sauti, kyakykyawan gudanarwa kuma na kwarai.

Makarfi ya lura cewa Hayatu-Deen ya samu nasarori a ayyukansa daban-daban musamman a kamfanoni masu zaman kansu. “Na gaskanta iko daga wurin Allah yake zuwa; duk da haka, na yi imani da cewa Hayatu-Deen zai iya kyakkyawan shugabanci,” inji shi.

Tun da farko, Mista Felix Hyet ya kuma bayyana Hayatu-Deen a matsayin mutum mai mayar da hankali kuma gogaggen mutum mai kyakkyawan tarihi.

Leave a Reply