Connect with us

Adabi

Na Rubuta Wannan Littafi Nawa Ne Kan Yadda Ake kiwo Don ‘Yan Uwana Manoma Su Amfana – Babangida

Published

on

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu.

A TATTAUNAWAR da wakilinmu na Jihar Yobe ya yi da Malam Babangida Ahmed Potiskum wanda masani ne a kan fannin kimiyyar dabbobi a garin Potiskum cikin Jihar Yobe, kuma marubucin littafin ‘Kiwo Da Yadda Ake Yin Sa’ za kuji yadda ya  bayyana dalilan da ya sa ya rubuta wannan littafin da harshen Hausa tare da sauran abubuwa. Asha karatu lafiya.

GTK: Akwai bukatar ka bayyana wa masu karatu takaitaccen bayani kan ka? 

Babangida:- To ni dai sunana Babangida Ahmed, kuma an haife ni a garin Potiskum da ke Jihar Yobe, kuma na fara karatuna na firamari a Jihar Filato wanda daga karshe na kammala a nan Jihar Yobe, kuma a nan na yi karatuna na sakandire, daga baya na tafi Jami’ar Maiduguri inda na yi digirina na farko a tsangayar ayyukan noma a bangaren kimiyyar dabbobi, wannan shi ne takaitacen tarihina a gurguje.

GTK- Ko me ya jawo hankalin ka har ka zabi karanta wannan fanni na kimiyyar dabbobi? 

Babangida:- “To da farko dai ban kudurci karanta fannin noma da kiyo ba, na nemi na zama Likita ne tun farko wanda a tashin farko hukumar tsara jarabawar share-fagen shiga jami’o’i  JAMB ta bani damar karanta fannin likitan, amma kuma na samu tangarda da ita Jami’ar Maiduguri, shi ne sai suka bani wannan fanni da na karanta. Sannan kuma a wancan lokacin na yi ta tunanin sake dawowa neman wancan fannin da na fi bukatar fannin karatun Likita, wanda a lokacin cike yake da kalubale, sai ya zama ban samu ba. Wanda a karshe na hakura da abin da ya samu, haka na dage har raina ya karbi zabin ala dole, tare da mayar da hankali a kai kuma sai na dauki hakan a matsayin zabin da Allah SWT ya yi mun.”

GTK:- To bayan kammala karatun digirin farko a wannan fanni, ka yi tunanin amfani da shi wajen bunkasa harkokin noma da kiwo? 

Babangida:- “Alal hakikia ba zan ce a tashin farko na yi wasu abubuwa dangane da habaka aikin noma kai tsaye ba, face a fakaice saboda kamar yadda kowa ya sani shi ne, bayan kammala bautar kasa (NYSC) sai na tsunduma a aikin jarida. Na dauki wannan fanni ne saboda yadda na kasance tun a farkon rayuwata ina sha’awar rubuce-rubuce ne matuka.”

“Kuma na fara ne da wata Jarida da na kafa mai suna ‘Jakadiya’, na fara buga shafi daya ina rabata a masallatan Juma’a da sauran ofisoshin ma’aikatan Gwamnati kyauta har na fara sayar da ita kama daga naira 5 zuwa 10 har dai ta habaka ta zama Jarida kuma daga bisani ta zama ‘Mujalla.’ Baya ga haka, da na ga tafiyar ta mike shi ne na yi tunanin samar da wata sabuwar ‘Mujalla’ (Magazine) ta Turanci mai suna ‘National Epitome’ wanda a yanzu haka ni nake tafiyar da ita (Publisher and Editor-inchief), amma duk da hakan ban jefar da wannan fage nawa na noma da kiwo ba, saboda na kan yi rubuce-rubuce a wasu Jaridu a duk fadin kasar nan, dangane da abubuwan da suka shafi noma da kiwo, musamman a Jaridun Hausa da wadanda nake yi. Baya ga wannan kuma Jama’a suna neman shawarwari daga gareni kan noma da kiwo a halin da ake ciki a yanzu.”

GTK:- Lura da cewa noma da kiwo na daga cikin manyan jigon ci gaban tattalin arziki, a matsayinka na kwararre, ya za ka danganta shi da Jihar ka ta Yobe kasancewar Jiha ce da mafi yawan al’ummar ta manoma ne kuma makiyaya?

Babangida:- “Alal hakika, noma da kiwo suna daga cikin abubuwa masu muhimmancin da ya dace Jama’a su kalle su da idon basira. Kuma kamar yadda ka bayyana cewa su ne jigon ci gaban tattalin arzikin kowace kasa, wanda bisa gaskiyar magana mu a nan Jihar Yobe, ana samun ci gaba ta wannan fanni, saboda duk mutumin da ya san yanayin rayuwar al’ummar wannan Jihar zai ga canji idan an kwatanta da shekarun baya.”

A baya kusan magabatan mu sun fi raja’a a harkokin noma, amma sakamakon ci gaba da wayewar da aka samu yanzu za ka tarar matashi ya zage dantse ga harkokin noma, kuma abin sha’awa shi ne yadda matashi kan noma amfanin da ya zarta yawan iyalin shi. Kuma sai ma ka tarar da matashi ya na noma buhuna daruruwa, abin gwanin ban sha’awa, idan mun dawo ta fannin Gwamnatin Jihar, musamman karkashin Gwamna Mai Mala Buni, za mu ga yadda ya yi shirye-shirye masu kayatarwa tare da bunkasa harkokin noma, saboda ina daya daga cikin wadanda Gwamnati ta tura nemo sahihan bayanai kan harkokin noma a karkashin Kwamishiniyar Ma’aikatar Noma, Dakta Hajiya Mairo Amshi, hakika na ga akwai ci gaba sosai idan an kwatamta da shekarun baya, wanda idan abin ya dore akwai dimbin nasarori.

To amma duk da haka akwai manyan kalubalen da manoma ke fuskanta su ne a halin da duniya ta ci gaba, harkokin noma sun wuce aikin fartanya ko hannu kamar da, akwai bukatar tafiya dai-dai da zamani, shi ne ya sanya na yi cikakken bayani a cikin littafin da na rubuta dangane da mayar da hankali wajen sauya salon yadda ake gudanar da noma daidai da zamani. Ka ga kenan akwai bukatar gwamnati ta tashi tsaye wajen kawo kayan noma na zamani tare da raba su ga manoma na gaskiya, kuma a guje aringizo a fannin, tare da tabbacin abin ya shiga hannun manoman gaskiya kamar yadda na ambata.

GTK:- Za mu so mu  ji bayanin abin da wannan littafi da ka rubuta ya kunsa ciki? 

Babangida:- A gaskiya shi wannan littafin da na rubuta wanda zancen da nake da kai yanzu ya karade lungu da sakon Najeriya tare da bayyana gamsuwa da alfanun da ya kunsa, musamman manomanmu a yankunan karkara da birane. Wannan littafi wanda na saka masa sunan: “Kiwo Da Yadda Ake Yin Sa” ya tattaro bayanan yadda ake kiwo ne a zamanance kuma a saukake, kuma ya zo ne sakamakon yadda na dauki dogon lokaci ina rubuce-rubuce a Jaridun kasar nan dangane da noma da kiwo, shi ne Jama’ar da ke bibiyar wadannan rubuce-rubuce su ka bukaci samar da littafin da zai kunshi bayanai dalla-dalla don amfanar da Jama’a tare da haskaka hanya a fannin kiwon wanda bayan nazari da na yi na amince da wannan bukata tasu kuma cikin taimakon Allah na yi nasarar wallafa shi a wannan shekara Kuma ya kunshi shafuka 168. 

GTK:- Wadanne kalubale ka fuskanta a yayin rubuta littafin da ma bayan kammala shi? 

Babangida:- To alal hakika, munsan a duk lokacin da ka kudurci aiwatar da wani abu na ci gaba dole ka hadu da kalubale, amma daga cikin kalubalen da na fuskanta akwai batun fassara kalmomin kimiyya na Turanci ko Girkanci zuwa Hausa, wannan ya bani wahala kwarai da gaske, musamman da yake ni ba Bahaushe ba ne. Kalubale na biyu shi ne batun kudin buga wannan littafi, wanda ya sanya na yi ta fadi-tashin nemo wata kungiya mai zaman kanta ko NGOs masu gudanar da harkokin noma da kiwo domin su dauki dawainiyar buga littafin su raba shi ga al’umma, amma abin ya ci tura- sannan kuma na bi duk hanyoyin da suka dace wajen neman Gwamnati don ta dauki nauyin buga littafin shi ma abin ya faskara. Dole ya jawo na shiga na fita wajen neman kudin da zan buga littafin da su kuma na sha wahala sosai kuma shi ne ya kawo tsaiko wajen fitar littafin. 

Kuma idan zan gaya maka adadin kudin da na kashe wajen buga littafin da kuma yadda ake sayar da shi a kasuwa za ka sha mamaki, saboda babu wata riba face kawai sadaukarwa ce. Kuma zan yi amfani da wannan dama na yi kira ga Gwamnatin Jihar Yobe a karkashin Gwamna Mai Mala Buni ya taimaka a dauki nauyin buga littafin tare da raba shi ga al’umma.

GTK:- Me ya ja hankalinka na rubuta littafin kuma ya baka sha’awar rubuta shi da harshen Hausa?

Babangida:- Babban abin da ya ja hankalina na rubuta wannan littafi da harshen Hausa shi ne idan ka duba kaso 80 cikin dari na manoma a wannan yankin na Arewacin Najeriya sun fi amfani da harshen Hausa a kan Turanci, kuma mafi yawan rubuce-rubucen da aka wallafa a wannan fanni a baya da harshen Turanci aka yi su. 

Kuma har yanzu babu wani canjin azo a gani da aka samu dangane da yadda ake gudanar da harkokin noma da kiwo. Sai na ga cewa su din nan, ko da a kasuwar dabbobi ka je za ka tarar cewa wadannan manoman ne wadanda ba sa jin Turanci ko magana dashi face Hausa. 

Abu na biyu kuma shi ne, har yanzu dai wadannan mutanen suna iya karatun Hausa na boko kuma za su iya karanta littafan amma ko bihin na Turanci bai sani ba, saboda haka za su yi maraba da wannan littafi. Wannan ya na daga cikin abubuwan da su ka ja hankalinka wajen rubuta wannan littafi da harshen Hausa. Sannan kuma kamar yadda na fada da farko, na wallafa shi ne domin taimaka wa al’ummarmu ta ci gaba tare da bunkasa harkokin tattalin arzikin Jihar mu da kasa baki daya.

GTK:- Yanzu da a ce Gwamnatin Jihar Yobe ta bukaci ta ba ka dama wajen sake wallafa littafin me za ka ce? 

Babangida:- “To a gaskiya in da zan samu haka lalle zan bai wa Gwamnatin Jihar Yobe cikakken goyon baya idan har za ta nuna sha’awar wallafa littafin tare da raba shi ga al’umma. Saboda dama babban burina shi ne ya shiga hannun manoma kuma ya amfane su sannan a samu bunkasar tattalin arzikin Jihar Yobe. Saboda haka ina maraba da kowane lokaci idan gwamnatin Jihar Yobe za ta bukaci in bata don wallafa wa ko kuma ta bukaci na fadada shi, zan yi nan take domin a samu karin amfanuwa a shirye nake, saboda babban burinmu shi ne a ci gaba a matsayin mu na ‘ya’yan Jihar Yobe masu kishin ci gabanta matuka.”

Ni ɗan jarida ne mai zaman kansa. Mawallafi kuma mai sharhi a lamarin yau da kullum.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Adabi

Ko kunsan ma’anar waɗannan kalmomi?

Published

on

  1. Ƙahon Dandi; Jin ɗumi kusa da wuta, musamman lokacin sanyi, ko ma duk lokacin da ake jin sanyin.
  2. Zunguru; Wani abu ne, dangin ƙwarya, mai ɗan tsayi da ake yi masa ƙofa daga sama a rarake cikinsa, mata kan cusa hannunsu a ciki zuwa guiwar hannu, bayan an zuba kwaɓaɓɓen lalle domin yin ƙunshi.
  3. Azargagi; Dogon zare ko tsumman da aka kekketa aka kuma ƙulla suka yi tsawo. Mata na amfani da shi wajen tufke ledar da suka naɗe ƙafafu da ita yayin ƙunsa lalle (kamar yadda yake a wannan labari, amma ya na da wata ma’anar ta daban).
  4. Mazari; Ɗan tsinke ne na Itace kamar tsintsiya, amma ya fi tsintsiya ƙwari, an haɗa shi da dunƙulen laka, ya na da tsini daga ƙasa. Ana amfani da shi wajen kaɗi ko murza auduga ta koma zare.

KU KUMA KARANTA: Flora Nwapa, jagorar mata adabin zamani na Afirka

  1. Taskira; Ɗan kwando ne ƙarami mai ɗan faɗi da ake saƙawa da Kaba, sannan sai a shimfiɗa masa ‘yan jemammun fatu a cikinsa. A saman fatar da aka shimfiɗa ake murza mazari wajen kaɗi. Mata kuma kan yi amfani da shi wajen ajiya, sai a ɗaga fatun a ɓoye abin da ake son ɓoyewa tsakanin fatun nan, wasu na kiransa “Tayani.” Akwai kuma wani ɗan kwando na Kaba mai marfi da ake sargafewa a jikin bango ana ajiya a ciki, wasu na kiransa “Taskira.”
  2. Abawa; Zaren da aka samar daga taffa (audugar da aka cire wa ‘ya’ya) ta hanyar kaɗi da mazari.
  3. Akwasa; Wani Itace ne da aka sassaƙa, ya na da tsayi da ɗan faɗi kamar dai Takobi. Mata na amfani da shi wajen saƙa.
  4. Gafaka; Jakar da aka yi daga fata domin adana littattafai.
  5. Agalemi; Fatar Akuya ko rago da ba a jeme ba har suka bushe (buzu).
  6. Akushi; Mazubin abinci da aka sassaƙa da Itace (kwanon cin abinci na Itace).
  7. Ƙoshiya; Cokali na Itace.
  8. Gidauniya; Ƙwaryar da ake zuba wa maigida fura a rufe da faifai.
  9. Tarde; Wani ɗan abu ne da ake saƙawa da kaba a zagaye kamar gammo. Ana ajiye Gidauniya a sama don kada ta ɓingire. Matan Fulani ma na amfani da shi wajen tallar nono, idan za su ajiye ƙwaryar nono sai su ajiye shi ƙasa, su girke ƙwaryar kansa.
  10. Jemo; Shi ne matsayin kofin shan ruwa a yanzu. Da ‘yar ƙaramar ƙwarya ake yinsa, girmansa kamar ɗan ƙaramin kwanon sha. Matan Fulani ma na amfani da shi wajen auna nono.
  11. Jallo; Ɗan goran duma da ake zuba ruwa idan za a yi tafiya.
  12. Shantu; Wani abu ne dangin ƙwarya, tsawonsa kamar tsawon hannu, daga yatsu zuwa kafaɗa, sai dai bai kai kaurin hannu ba. Ana yanke kowane ƙarshe nasa, a rarake cikinsa, kamar dai ɗan guntun fayil na ruwa. Mata na amfani da shi wajen rera waƙoƙi. Su na buga shi a kan cinya su kuma riƙa kaɗa shi da ‘yan yatsun hannu, musamman idan an sa zobba ga yatsun, sai ya dinga ba da sautuka masu daɗi kamar ana kaɗa ƙwarya.
  13. Jaura; Lokacin da ya fi kowane lokaci sanyi yayin sanyin hunturu.
  14. Kindai; Ɗan ƙaramin kwando na Kaba mai marfi, wadda mata ke ajiya a ciki.
  15. Farsa; Ɗaya daga cikin sunayen goro kamar daushe, gandi da sauransu.
  16. Albada; Sautu ko saƙo.
  17. ‘Yar shara; Rigar da Bahaushe ya fara ƙirƙira. Riga ce mara hannaye.
  18. Kurtu; Kamar ‘yar kwalba ko ɗan gwangwani ke nan a halin yanzu, amma wannan na Duma ne. Yawanci ana zuba tawadar rubutu a ciki. Haka tsoffi kan ajiye shi a cikin ɗaki domin zuba yawu. Har a wasu masallatai ma a kan ajiye shi domin zub da yawu a da can.
  19. Ala; Baki ya yi ja idan an tauna goro ba a haɗiye ba.
  20. Ruɗa-kuyangi; Rana ta yi ja za ta faɗi.
  21. Kwiɓin bazawara; ‘Yar siririyar hanyar ƙauye, musamman wadda ake tafiya da ƙafa, takan ɗan yi zurfi kuma ciyawa kan fito gefe da gefe. To gefen hanyar shi ne kwiɓin bazawara, wadda idan mai keke ko mai babur ya kuskure tsakiyar hanyar ya taka gefe, santsin ciyawar zai iya kayar da abin hawansa.
  22. Mayani; Ƙyalle ko tsumma da tsoffi ke ƙulle wani abu a ciki.
  23. Tsariya; Ƙarƙashin gado, musamman irin gadon dauri da akan yi na ƙasa sai a yi ‘yar ƙofa daga ƙasa wadda ake sa wuta lokacin sanyi, sai gadon ya yi ɗumi a ji daɗin kwanciya. Yanzu da babu irin wancan gadon, ƙarƙashin kowane irin gado ana iya kiransa tsariyar gado.
  24. Asabari; Kamar labulen ƙofa ne da ake yi da siraran kara ko gamba ko wani abu daban. Ana saka shi daga wajen ƙofa, yawanci domin kare feshin ruwa ko rana.
  25. Hirji: Addu’a ko neman kariya daga wani abin da ake tsoro.
  26. Amaryar wata; Sabon wata, kwanakin farko na wata.
Continue Reading

A Gani Na

Burina a tuna dani a marabucin da ke nusar da shugabannin – Hassan Gimba burin a tuna ni a marubucin dake nusar da shugabanni – Gimba

Published

on

“Tun Ina aji ukun firamare na ke karanta wa mutane litattafan Hausa”

Dr. Hassan Gimba ƙwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru sama da 30 yana aikin jarida. Ɗan asalin garin Potiskum dake Jihar yobe, sannan mamallakin kamfanin jaridun Neptune Prime. A cikin wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu Abubakar M. Taheer, ya kawo irin nasarorin da ya samu a cikin aikin dama irin matsalolin da aikin na jarida yake fuskanta a yanzu. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu.

DAKTA HASSAN: Assalamu alaikum warahamatullah. Ni dai sunana Hassan Gimba haifaffen garin Potiskum dake Jihar yobe.
Tun tasowa Ina da sha’awar karance-karance tun Ina aji uku na firamare. Zan iya tunawa ‘yan’uwana da ƙannena sukan zagaye ni, Ina karanta musu littafin ‘Magana Jari’, ‘Ruwan Bagaja’ da Iliya Ɗan mai Ƙarfi’. A zamanin babu television sai dai a kunna fitilar ƙwai Ina karanto musu suna saurara.

Bayan nan dana shiga aji huɗu da biyar na firamare Ina karanta jarida, da yake mahaifinmu ɗan boko ne yakan dawo gida da jaridu kamar kowanne ɗan boko kan yi, jaridu kamar ‘Time magazine’, ‘Readers Digest’ da dai sauran su. Ni kullum yana dawowa na kan karɓa ne na karanta.
Nakan karanta jaridun daga bango zuwa bango nake karantawa. Da na shiga aji shida na kan siyi jaridun da kaina. A lokacin Idan zan tafi makaranta akan bani Sile goma, su kuma jaridun ana siyar su Sile ɗaiɗai ne.
A haka sai na siyi jaridun guda goma kala-kala Ina tahowa da su, Ina karantawa. A haka dai har ya zama na koyi karanta jarida dama na iya Turanci sosai.

Waɗanne ƙalubalai za a ce ka fuskanta ganin irin daɗewar da ka yi kana aikin na jarida?

To kasan ƙalubale kala-kala ne, kusan zan iya cewa kowa da yadda yake kallo ƙalubalai. Misali yawanci ‘yan jarida akwai fama da rashin kuɗi, wato rashin albashi don haka mutum yana ganin labari mai kyau don rashin kuɗi sai ya zama ba shi da
damar zuwa ya ɗauko ba. Wani lokacin ka fita daga gida ba abinci baka da kuɗin komowa gida a haka sai ya zama mutum ya kasa ɗaukan labari. Haka kuma ada za ka rubuta labari ka ɗora a mota akai hedkwatarku, amma a yanzu za ka ga ana amfani da na’urori na zamani wanda rashin su kan hana ‘yan jaridu gudanar da aikinsu.

Da yawa daga cikin matasa suna son cimma nasara a rayuwa cikin ƙanƙanin lokaci,don haka suna kallo irinku a matsayi makwafi. Ko ya abin yake?
To a gaskiya ita rayuwa babu wani abu da ake samun sa a sama, sai anyi aiki. Yawanci waɗanda suke kallo ko suke son cimma nasara cikin ƙanƙanin lokaci suna da ƙaranci ilimin zamantakewa. Ko ɗan sarki ne baya samun sarauta sai ya yi aiki tuƙuru. Da farko sai ya koyi ilimin zama da mutane, girmama manya da kuma sanin ilimin shugabantar jama’a. Wannan ne zai ba shi dama mutane su ga ya kamata su zaɓe shi.

Duk wanda ya fara wani abu daga sama, to ba zai jima ba zai ruguje. ko kuɗi ne, sai mutum ya fara da yaron shago, kwana a ɗaki ɗaya har Allah ya yi ya zama hamshaƙin mai kuɗi. Idan malinta ce sai ka fara da ƙolonta har zuwa farfesa.
Haka shima a aikin na jarida dole za ka fara da bin manya kana koya har ya zama ka iya. Misali ka ɗauka ni, yanzu haka Ina da shekaru kusan 31 a aikin jarida.

Nasarori fa za mu su mu ji waɗanne ka samu?

To alhamdu lillah. Kasan ita nasara kowa da abinda yake kallo a matsayin nasara. Ni ta nawa janibin ta wannan aikin na yi aure na hayayyafa a aikin nake ciyar da kaina da iyayena da iyalaina dama tallafa wa marasa ƙarfi. Kuma iya gwargwado Ina gode wa Allah kan hakan.
Bayan aikin jarida kenan kana da wata gidauniya ta tallafa wa marasa ƙarfi?

Eh, alhamdu lillah, zan ce Ina da gidauniya guda biyu ta taimaka wa al’umma. Na farko Ina da gidauniya mai sunan matata wanda ta rasu sanadiyyar sanƙarar mahaifa shekaru huɗu da suka wuce, wanda muke tallafa wa masu fama da wannan cutar da ba su magani ajin farko tare da wayar musu da kai kan haɗarin cutar.

Akwai rubuce-rubuce da nake yi a jaridar Blueprint da NewNigeria da wasu jaridun ‘online’ sun kai tamanin da wani abu inda muka tattara shi rubutun ya zama littafi guda biyu. Aka ƙaddamar da su, kuɗin da aka samu yanzu haka mun fara gina asibitin masu fama da cutar kansar mahaifa.
Haka kuma Ina da gidauniya da na buɗe mai sunan Abokina Ɗan Jarida Abubakar Monja wanda muke tallafa wa iyalan ‘yan jaridun da suka rasa ransu sanadiyyar harin Boko Haram da sauran haɗarori.

A shekarar 2007 Dakta ya fara shiga harkar siyasa. Shin aikin jarida ne ya kaika wannan matsayin ko yaya lamarin ya kasance?

Eh abinda zan ce shine, a shekarar 2007 na shiga harkar siyasa gadan-gadan a lokacin da wani aminina Tijjani Musa ya yi gwamna a Yobe, ya nemi na taimaka masa inda na fito takarar sanata a Jam’iyyar AC.
Bayan wannan kuma ina ga ban sake shiga harkar siyasa ba sai dai na marawa ‘yan siyasa baya waɗanda za su tallafa wa al’umma, Ina nufi ni nakan bi mutum ne ba jam’iyyar.

A ‘yan shekarun baya- bayan nan, ka buɗe kamfanin jaridarka na ‘Neptune Prime’ da ke yaɗa labarai da ‘online’. Waɗanne nasarori za a ce an samu daga buɗewa zuwa yanzu?

To alhamdu lillah. zan iya cewa, bayan na zama ‘reporter’ a jaridu da dama kamar ‘Today Newspaper’, ‘Daily monitor’, ‘This day’ da sauran su, sai na koma gida Potiskum na yi wata jarida Informant muka samu shekaru.

Daga nan sai na koma Abuja muke buga ‘Pen Watch’ a 2008 a lokacin muna bugawa tare da ‘Leadership’ a kamfani ɗaya.Daga nan sai na dawo ‘Leadership’ na zama edita nata, bayan zama edita daga nan minister na ‘Science and Technology’ a shekarar 2004 ya neme ni na zame masa S.A kan ‘Media and Publication’.

Daga nan na sake dawo wa Leadership Friday na zama editan inda na bar su a shekarar 2016. A shekarar 2017 a April sai na buɗe kamfanina na ‘Neptune Prime’ wanda muke watsa labarai online. Inda a bara na buɗe Neptune Prime Magazine, bana kuma muka fara talabijin na Neptune Prime.
Waɗanne abubuwa ka ke so ace al’umma ta tuna da kai da shi a matsayinka na tsohon ɗan jarida?

To alhamdu lillah, zan iya cewa kusan kowa za ka ga yana da abinda yake so ace bayan rayuwarsa an tuna da shi haka nima. Ina fatan ace wannan kamfanoni nawa na jarida ace ko bayan raina su ci gaba da gudana domin jama’a su tunani a matsayin marubuci wanda yake rubutu kan rayuwar ɗan adam da nusar da shuwagabanni yadda ya kamata su jagoranci al’ummarsu.
Wane kira ka ke da shi ga matasan ‘yan jarida da ma matasa bakiɗaya kan cimma nasara a rayuwa?

To alhamdu lillah, kira na da nake da shi ga matasa shine, su zamanto masu haƙuri. Kusan al’adar matashi shine rashin haƙuri, kusan idan ya ga wani babba yana da burin ace ya cimma sa.

Ba a samun haka sai anyi haƙuri an kuma yi aiki tuƙuru yau da gobe ana samun shekaru har Allah Ya kai ka kan wannan matsayin.

Idan ka duba za ka ga wani ya ɗauki shekaru20, 30 waje cimma nasararsa, amma matashi kullum ya rinqa tashi da jin cewa, yana son yin daidai wannan. Haƙuri da jajircewa na taimaka wa wajen cimma nasara a rayuwa.

Aikin jarida yana fuskantar barazana sakamakon bayyanar kafafen sada zumunta. Wane kira ka ke da shi musamman ga ‘yan jarida kan aikinsu?

To a yanzu gaskiya sakamakon bayyanar kafafen sada zumunta da mutum ya samu data shima ya zama ɗan jarida. Wanda kuma lallai ba haka abin yake ba, aikin jarida aiki ne da yake da tsari yake da manufofi ba kamar na sada zumunta ba.
To dole ɗan jarida ya zama yana kan wannan tsari domin ya bambanta da ɗan ‘social media’. Ya zama yana rubutu domin ƙaruwar al’ummarsa da ma duniya bakiɗaya.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like