Mutune 5 Sun Mutu, 10 Sun Bata A Wani Hari Da Aka Kai A Jihar Benue

1
260

Daga; Rabo Haladu.

AƘALLA mutum biyar aka gano gawarsu bayan wani kazamin harin ‘yan bindiga a karamar hukumar Guma da ke Jihar Benue.

Haka kuma mutum 10 suka ɓata, yayin da aka kaddamar da binciken ganosu.

Shugaban karamar hukumar Guma, Caleb Aba, ya shaidawa manema labarai cewa harin ya auku ne a yammacin ranar Litinin din da ta gabata.

Ya ce cikin mutanen da harin ya ritsa da su, akwai dilolin katako da suke aikinsu a wani jeji da ake kira Mbagwen.

Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da hari, tare da shaida cewa suna kan bincike mai zurfi a yanzu haka.

1 COMMENT

Leave a Reply