Ma’aikatar Yada Labarai Ta Lashe Gasar Kofin Ma’aikatun Jihar Kano

0
255

Daga; Mustapha Imrana Abdullahi.

BAYAN kammala gasar cin kofin da aka sanya wa ma’aikatun Gwamnati a Jihar Kano, ma’aikatar yada labarai ta Jihar, ta samu nasarar lashe kofin da aka sanya a Gasar.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar bayanin da ke dauke da sa hannun Abdul Umar Farouk babban mai ba Gwamnan Jihar Kano shawara a kan harkokin yada labarai.

An mika kofin gasar ga kwamishinan ma’aikatar yada labarai ta Jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba.

Leave a Reply