Connect with us

Ƙasashen Waje

Musulmai sun raba kwafin Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a Netherlands

Published

on

An raba wa jama’a Alƙur’ani da aka fassara da harshen Dutch a ƙasar Netherlands a wani shiri na ƙarfafa gwiwar ’yan ƙasar kan su riƙa karanta littafai masu tsarki maimakon ƙona su.

Shirin yana zuwa ne wata guda bayan jagoran ƙungiyar PEGIDA wanda ke ƙyamar Musulunci ya wulaƙanta Alƙur’ani.

Galip Aydemir, shugaban Gidauniyar Masallacin Arnhem Türkiyem wanda ke haɗin gwiwa da Gidauniyar Dutch Diyanet, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa suna ƙoƙarin isar da saƙo ga jama’a kan abin da ya sa addinin Musulunci da Alƙur’ani suke da daraja ga Musulmai.

Muna so a samu haɗin kai da ’yan’uwantaka tsakanin mazauna birnin Arnhem, in ji shi, inda ya ƙara da cewa: “Ya kamata a daina ƙona Alƙur’ani da sauran littafai masu tsarki, a riƙa karanta su ne.”

KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ta girgiza garuruwan Saudiyya, Iran, Masar da Lebanon saboda wulaƙanta Alkur’ani a Sweden

John Maters, wani ɗan Netherlands wanda ya samu kwafin Alƙur’anin ya yi godiya ga waɗanda suka shirya taron kuma ya soki waɗanda suka jagoranci wulaƙanta Alƙur’ani a watan da ta gabata.

“Abin da ya faru watan da ya gabata zai sa mutane su ƙara ƙin junansu ne. Ba na tunanin cewa sai mutumin da ya damu da addini zai fahimci cewa hakan rashin hankali ne,” in ji shi.

Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Shugabar Tanzania ta kori wasu ministocinta daga aiki

Published

on

Shugabar Tanzania ta kori wasu ministocinta daga aiki

Shugabar Tanzania ta kori wasu ministocinta daga aiki

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta sallami sanannun ministocinta biyu a wani ɓangare na garambawul ga majalisar zartarwa, kamar yadda daraktar riƙo ta sashen sadarwar fadar shugaban ƙasa, Sharifa Nyanga ta bayyana.

Korar Ministan Harkokin Waje January Makamba da Ministan Sadarwa, Yaɗa labarai da Fasahar Sadarwa, Nape Nnauye na zuwa a yayin da ake yaɗa jita-jitar suna yin wani yunƙuri cikin sirri na ƙalubalantar sake zaɓar Samia. Shugaba Samia ta hau kan mulki bayan rasuwar Shugaba John Magafuli.

A wata sanarwa da Sakataren Gwamnati Moses Kusiluka ya fitar a ranar Lahadi, an bayyana Mahmoud Thabit Kombo, ɗan majalisar dokoki a matsayin Ministan Harkokin Waje da Ƙawancen Gabashin Afirka. Kafin wannan muƙami, Kombo ne jakadan Tanzania a Italiya.

Sanarwar ta ce Jerry Silaa zai maye gurbin Nnauye a matsayin Ministan Sadarwa, Yaɗa Labarai da Fasahar Sadarwa. A baya Silaa na riƙe da muƙamin Ministan Ƙasa, Gidaje da Tsugunar da Jama’a.

KU KUMA: Burkina Faso ta kori jami’an diflomasiyyar Faransa uku bisa zargin ‘zagon ƙasa’

An naɗa Deogratius John Ndejembi a matsayin sabon Ministan Ƙasa, Gidaje da Tsugunar da Jama’a. Kafin naɗin nasa, shi ne Ƙaramin Minista a ofishin Firaminista.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an naɗa Ridhiwani Kikwete a matsayin Ƙaramini Minista a ofishin Firaminista. Kafin naɗin nasa, Kikwete ya yi aiki a matsayin Mataimakin Minista a sashen Ayyukan Gwamnati na Ofishin Shugaban Ƙasa.

Cosatto Chumi ya zama sabon Mataimakin Ministan Harkokin Waje, inda ya maye gurbin Mabrouk Nassor Mabrouk, wanda aka bai wa wani sabon muƙamin.

An naɗa Deus Clement Sangu a matsayin Mataimakin Minista a sashen kula da ingancin ayyukan gwamnati na ofishin Shugaban Ƙasa.

Dennis Lazaro Londa ya zama Mataimakin Firaministan Harkokin Waje da Ƙawancen Gabashin Afirka, wanda ya maye gurbin Stephen Lujwahuku Byabato, wanda aka sauke daga muƙaminsa.

Kazalika shugabar ƙasar ta yi wa wasu manyan jami’an gwamnatin sauyin wuraren aikin waɗanda suka haɗa da manyan sakatarori, shugabannin gundumomi, inda Eliakim Chacha Maswi ya zama Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Kundin Tsarin Mulki da Shari’a, sai Mary Gaspar Makondo da aka naɗa a matsayin Sakatariyar Gwamnatin Yankin Ruvuma.

Garambawul ɗin na nufin nuna ƙarfin ikon shugabar a yayin da ake tunkarar zaɓe a Tanzania a shekara mai zuwa.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Joe Biden ya janye daga takarar shugaban Amurka

Published

on

Joe Biden ya janye daga takarar shugaban Amurka

Joe Biden ya janye daga takarar shugaban Amurka

Shugaban Amurka Joe Biden ya janye daga neman sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar bayan wasu ‘yan jam’iyyarsa ta Democrat sun matsa masa lamba don ya hakuri da takarar sakamakon rashin cikakkiyar lafiyar kwakwalwa.

A wani saƙo da Biden ya wallafa a shafin X, ya ce zai ci gaba da ayyukansa na shugaban Amurka kuma babban kwamandan tsaron ƙasar har ƙarshen wa’adin mulkinsa na farko a watan Janairun 2025 kuma zai yi wa ‘yan ƙasar jawabi a wannan makon.

“Abin alfahari ne a gare ni da na kasance shugaban Amurka. Ko da yake na yi niyyar sake tsayawa takara, na yi amanna zai fi kyau ga jam’iyyata da kuma kasar nan na janye daga takara sannan na mayar da hankali wurin aiwatar da ayyukana na shugaban ƙasa a ragowar wa’adina,” in ji Biden.

KU KUMA KARANTA: Amurka ta ja hankalin ‘yan siyasar Isra’ila da su kiyayi rura wutar rikici tsakanin su da Falasɗinu

A wani saƙo na daban da ya wallafa a shafin X, Biden ya goyi bayan Mataimakiyar Shugaban kasa Kamala Harris domin neman takarar shugaban Amurka a jam’iyyarsu ta Democrat.

“Matakin farko da na dauka bayan jam’iyya ta tsayar da ni takara a 2020 shi ne na dauki Kamala Harris a matsayin mataimakiyar shugaban kasa. Kuma wannan shi ne mataki mafi muhimmancin da na dauka,” a cewarsa.

Ya ƙara da cewa, “A yau, ina bayar da dukkan goyon bayana ga Kamala domin zama ‘yar takarar jam’iyyarmu a wannan shekarar. ‘Yan Democrat — lokaci ya yi da za mu hada kai domin kayar da Trump.”

Harris za ta kasance mace bakar-fata ta farko da za ta yi takarar shugaban Amurka a tarihi.

A martanin da ya mayar, Trump ya shaida wa CNN ranar Lahadi cewa yana ganin Harris za ta fi saurin kayarwa fiye da Biden a zaben da za a gudanar a watan Nuwamba.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

An kama jirgin ruwa ɗauke da ‘yan ci-rani sama da 200 da ke hanyar zuwa Turai

Published

on

An kama jirgin ruwa ɗauke da 'yan ci-rani sama da 200 da ke hanyar zuwa Turai

An kama jirgin ruwa ɗauke da ‘yan ci-rani sama da 200 da ke hanyar zuwa Turai

Rundunar Sojin Senegal a ranar Asabar ta ce ta kama wani jirgin ruwa wanda ke ɗauke da ‘yan ci-rani sama da 200 waɗanda ke hanyarsu ta zuwa Turai.

A wata sanarwa da sojojin suka fitar a shafinsu na X, sun bayyana cewa wani jirgin ruwan soji wanda ke shawagi ne ya gano jirgin a ranar Juma’a ɗauke da mutum 202, daga ciki har da mata biyar da ƙaramin yaro.

A farkon watan Yulin nan, wani jirgin ruwa ɗauke da kusan mutum 170 wanda ya bar Senegal zuwa Mauritania ya kashe kusan mutum 90 bayan ya kife.

Wannan bala’in ne ya jawo Firaiministan Senegal Ousmane Sonko ya yi magana da babbar murya inda ya roƙi mutane da su daina kasada suna sayar da rayuwarsu ta hanyar shiga irin waɗannan jiragen ruwan masu cunkoso.

Sai dai duk da haka masu tafiya ci-ranin zuwa Turai a halin yanzu suna ƙara bin wannan hanya duk da yadda ake ƙara tsaurara tsaro a cikin tekun.

KU KUMA KARANTA: Wani jirgin ruwa ya kife da ‘yan ci-rani a tekun Mauritania

“Ina sake kira ga matasa: ba za ku magance matsalolinku a cikin jirgin ruwa ba,” kamar yadda Sonko ya shaida wa taron wasu matasa a Saint-Louis.

“Makomar duniyar nan ita ce Afirka… wadda ita ce nahiyar da har yanzu take da akamun samun ci gaba.”

Kamar yadda wata ƙungiya mai zaman kanta ta Sifaniya Caminando Fronteras ta bayyana, sama da mutum 5,000 suka rasua hanyarsu ta zuwa Sifaniya ta teku a watanni biyar na farkon wannan shekarar, wanda wannan shi ne adadi mafi yawa tun bayan da ƙungiyar ta soma aikin tattara alƙaluma a 2007.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like