Matsayar Jam’iyyar APC Na Tsayar Da Yan Takara Musulmai Ba Shi Ne Mafita Ba – Kungiyar NNFEGG

0
337

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna

WATA Kungiyar da ke fafutukar tabbatar da daidaito da shugabanci nagari a Arewacin Najeriya wato Northern Nigeria Front For Equity And Good Governance (NNFEGG), ta bayyana cewa matsayar da Jam’iyyar APC ta dauka na zabar dan takarar Shugaban Kasa Musulmi da mataimakinsa Musulmi ba shi ne mafita ga Jam’iyyar da al’ummar kasar baki daya ba.

A wani taron manema labarai da Kungiyar (NNFEGG) ta gudanar a ranar Juma’a a sakatariyar Kungiyar Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, Shugaban Kungiyar Zakariya Abdul-Aziz, ya bayyana cewa yin irin hakan wani nau’in nuna rashin adalci ne ga al’ummar kasar Najeriya ne.

Ya kara da cewa, duk wata Jam’iyyar siyasar da ke da irin wannan manufar na tsayar da yan takara masu irin alkilbar addini iri daya a matsayin Shugaba da mataimakinsa tamkar yadda Jam’iyyar APC ta yi a yanzu, wata alama ce da ta ke nuna kalibancin addini karara, wanda kuma yin hakan ke nuni ga nasabar samun rashin nasara agare ta a babban zabe mai zuwa ta shekarar 2023.

Shugaban Kungiyar (NNFEGG), Malam Zakariya, ya kara shaida cewa a matsayinsu na masu kishin ci gaban Kasar da al’ummar kasar baki daya, ba zasu laminta da irin wannan tsarin ba musamman daga Jam’iyyar APC mai mulki a yanzu, domin yin hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

Ya ce “idan har ana da bukatar daukar wani daga Arewacin Najeriya domin yin daidaito, to kamata ya yi a samu wani wanda ya dace kuma ya cancanta daga cikin kiristocin Arewa, saboda yin hakan shi ne adalci ga al’ummar kasar da su kiristocin koda ko an zabo ne daga cikin al’ummar kirista wadanda suke marasa rinjaye.”

“Muna da mutanen da an aminta da irin salon mulkinsu da jajircewa kamar irinsu Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong wanda shi ne ke shugabantar Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF), kuma kowa yasan kirista ne amma aka amince da irin dacewarsa da cancanta bisa jagorantar wannan matsayin.”

“To babu shakka, muddun har za a iya samun irin wannan mutumin a Arewa, to ya kamata a daauke shi a matsayin abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC domin
irin wannan zai dore da daidaiton siyasar da ake yi a yanzu ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.”

Kungiyar ta nuna damuwar ta matuka bisa kalaman wasu ‘yan tsiraru da suka yi yunkurin yin amfani da addini da kabilanci a fake da cewa suna yi wa yankin Arewa jawabi a kan zaben ‘yan takarar siyasa da abokan takararsu.

Kungiyar ta fusata kan tikitin Muslim -Musulmi a matsayin hanya daya tilo ta samun nasara ga jam’iyya mai mulki kamar yadda wasu ‘yan tsiraru suka bayyana ra’ayinsu, alhalin yin hakan za ta iya zama wata hanyar yunkurin ruguza hadin kan al’umma gami da daidaito wanda aka kafa.

A cewar kungiyar, an san Arewa ce a sahun gaba wajen bunkasa siyasar dunkulewa a kasar nan, don haka akwai bukatar samun adalci da daidaito ta hanyar yin watsi da kiraye-kirayen da wasu ke yi na tsayar yan takarar duk Musulmai ko Kiristoci.

A karshe, Kungiyar (NNFEGG) ta yi kira da al’ummar kasar da su kwantar da hankulansu, kana ta kara da jaddada yin kira ga shugabannin addini, siyasa da al’ummar Arewa a kan su fito su nuna rashin amincewar su bisa wannan tsarin ta hanyar dakatar da shi domin gujewa haifar da rudani a Arewacin Najeriya.

Leave a Reply