Matashi ya hallaka budurwarsa da sarar adda, saboda ta fasa wayarsa ƙirar IPhone

0
430

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Jami’an tsaro sun cika hannu da wani matashi ɗan shekara 23, mai suna Godspower Adegheji da laifin kashe budurwarsa mai suna Gift Oloku mai shekara 22, bisa laifin karya wayarsa ƙirar IPhone 11 pro max a Etevie quarters Ozoro, ƙaramar hukumar Isoko ta Arewa a jihar Delta.

Cikin wata sanarwa da jami’an hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, Bright Edafe, ya fitar ta bayyana cewa masoyan sun kaure da fada ne a lokacin da lamarin ya faru.

An tattaro cewa maharin ya aikata abinda ya aikata ne lokacin da shi Godspower ya tambayi dalilin da yasa budurwar tasa Gift ta bar gidansu ba tare da ta sanar dashi ba bayan ta lalata masa wayarsa.

Bisani wanda ake zargin ya yi amfani da adda ya bugi Gift, ta lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ta nan take.

Leave a Reply