Matasan Arewa Sun Yi Kira Ga Gwamna Emmanuel Ya Fito Takarar Shugaban Kasa A 2023

0
267


Gamayyar kungiyoyin cigaban matasan Arewa a mahanga ta gaskiya da suka kunshi (Northern Youth for Good Governance da Arewa Political Awareness Initiative da Mufarka Arewa Youth Political Vanguard) sun bukaci Gwamnan jihar Akwa Ibom Mista Udom Emmanuel da ya gaggauta bayyana fitowarsa takarar shugaban kasa a zaben 2023 dake tafe.
Babban sakataren kungiyar na kasa Bishir Dauda ne ya bayyana hakan a Abuja. Magaji ya bayyana cewar a halin da ake ciki Najeriya na hukatar haziki, Jarumi kuma jajirtacce wanda zai ceto Najeriya daga halin da take ciki, a cewarsa ba kowa bane ya cancanci zama shugaban Najeriya na gaba kamar Gwamna Emmanuel na jihar Akwa Ibom. 
“A halin da Najeriya take ciki yanzu, gibin dake tsakanin masu mulki da wadan da ake mulka wagege ne, Najeriya na bukatar mutum mai kwazo da zai iya hade kan alummar Najeriya domin bayar da jagoranci na gari abin misali ” 
“A matsayinsa na kwararre akan harkokin tasarrufi da kudade, kuma Gwamnan da ya jagoranci jihar Akwa Ibom kuma ta samu cigaba mai ma’ana, irin wannan mutum ne ya dace da shugabancin Najeriya a zabe na gaba mai zuwa.
“A saboda haka wannan gamayya ta kungiyoyin cigaban matasan Arewa a mahanga ta gaskiya ta hanga ta hango Gwamna Udom Emmanuel a matsyin mafita ga Najeriya a shekarar 2023” a cewar Bishir Dauda.

Leave a Reply