Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.
WATA kungiyar Dattawa Yan kishin Arewacin Najeriya mai suna “Arewa Elders Initiatives and Interactive Group,” sun yaba da irin matakan da Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle, ya dauka domin yin maganin masu zagon kasa da suke bayar da bayanai ga yan bindiga, wanda dalilin hakan ke haifar da ci gaba a batun matsala kawo karshen ayyukan yan bindigar daji da sauran miyagun ayyuka na rashin tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
‘Ya’yan Kungiyar, sun bayyana hakan ne a cikin wata takardar bayani ta bayan kammala taron tattaunawa da suka yi da wasu zababbun yan kungiyoyi masu rajin kare Arewa dake zaman kansu, taron an yi masa taken; ‘ Kalubalen da ke fuskantar Arewa maso Yamma da kuma batutuwan da suke a baya na irin nasarar da ake samu wajen yaki da masu satar jama’a da ayyukan yan bindiga gabanin zaben 2023’.
Shugaban wannan Kungiya ta kasa Masanin Hallayar ‘Dan-Adam Honarabul Alhassan Ado Gwadabe ya bayyana cewa sababbin hanyoyin da Gwamna Bello Matawalle ya dauka a baya da na yanzu a Jihar Zamfara sun hada da kama masu bayar da bayanai ga yan Ta’adda (Informants), rufe dukkan layukan wayoyin Sadarwa, hana sayar da mai da tona asirin masu hada kai da yan bindiga ko masu satar jama’a da suke a cikin al’umma da kuma rushe dukkanin wurarensu, da kuma cire masu sarautar gargajiya da shugabannin al’umma da ake zargi da hada baki ko kuma yin sakaci da aikin tabbatar da samar da zaman lafiya a yankin da suke.
Ya’yan Kungiyar, sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari, da shugabannin rundunonin tsaro da Gwamnonin yankin da su samar da wadansu dabarun da za su ci gaba da taimakawa wannan yankin da ake da yan bindiga masu satar mutane da ke addabar Jama’ar yankin baki daya, musamman ma da irin rahotannin da ake samu a halin yanzu na kara bazuwar ayyukan yan Ta’adda da suke kashe Jama’ar da ba su ji ba su gani ba a wasu yankunan Jihohin Kaduna, Neja da Kebbi.
Ya’yan Kungiyar, sun tabbatar da cewa a watanni biyu da suka gabata, Jihohin Neja, Kaduna da Kebbi, sun rasa mutane akalla dari biyu a sakamakon yawan hare-haren ta’addanci da ake samu da ake zargin yan ta’adda ne da suke yin ta’addanci a yankunan Kaduna da Jihar Neja da suke samun goyon bayan sirri daga wasu bata gari a cikin al’umma.
“Babban kalubalen da ake samu a wajen yaki da yan bindiga wadanda a yanzu aka bayyana a matsayin yan Ta’adda shi ne a halin yanzu a canza salon yaki da wadanan miyagun ta yin amfani da irin salon da Gwamnan Jihar Zamfara, Honarabul Muhammad Bello Matawalle ya dauka da ake cewa ‘Gama aiki’ na kama masu bayar da bayanan sirri (Informants) aiki da shugabanin jama’a da kuma hanyoyin siyasa, bayar da dukkan taimakon da masu aikin Sa-kai ke bukata da suka hada da kayan aiki da nuna masu goyon baya ga sauran jami’an tsaro da suke aikin kokarin maganin yan ta’adda.
Sauran mahukunta na kasa suyi koyi da salon da Gwamnatin Jihar Zamfara ta dauka na haifar da samun nasara, domin ana tona asirin masu bayar da bayanai a duk inda maboyarsu take, da kuma samun wadansu hanyoyi na musamman wajen yaki da yan bindiga da nufin magance matsalolin tsaro, wanda hakan ya haifar da samun nasara domin an samu raguwar matsalar ba kamar yadda abin yake a can baya ba, illa a wasu wurare da ake ganin ana yiwa barazana.
Hakika da akwai nasara wanda hakan ya samar da samun yanayin zaman lafiya da har mutane ke samun walwalar gudanar da ayyukansu da kuma tafiya daga nan zuwa can a wuraren da a can baya suka yi kaurin suna na ba mai iya zuwa wajen.
Kuma sakamakon rahotannin da aka samu inda mutane sama da miliyan biyu suka taru a cikin babban birnin Gusau, daga Jihohin Najeriya dabam dabam na tsawon kwanaki uku domin yin harkokin al’amuran addini ba tare da samun wani barazana na rahoton kama wani ko satar wani ko wasu ba; hakika abin ya na karfafa gwiwa kwarai domin ana samun ci gaban zaman lafiya sannu a hankali duk da akan samu wadansu yan matsalolin a wasu wurare nan da can.
Don haka, muke bayanin cewa akwai yuwuwar samun hadin kai, fahimtar Juna, amincewa da samun bayanan sirri a tsakanin dukkan hukumomin tsaro da suke cikin wannan aikin da al’umma da nufin daukar matakan da za su kawo nasara.
Saboda daukar matakin soja kawai ba zai yi maganin wannan matsalar ba ta kashe mutane da bata dukiyar jama’a tare da salwantar rayukansu.
Don haka Kungiyar ta Dattawan Arewa ta bayar da shawara ga Gwamnonin Jihohin Kebbi, Neja,Kaduna, Zamfara, Sakkwato da Katsina da su shirya wani babban taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Gusau domin tattauna muhimman batutuwa baki daya da nufin gano wadannan kalubalen gabanin fara ayyukan siyasar shekarar 2023 mai zuwa.
Haka ma Kungiyar tayi Allah wadai da irin zargin goyon baya da wasu sannanun yan siyasa da manyan yankin Arewa ke nuna wa ga wasu da aka kama ko suke tsare a a hannun Hukuma ana bincikensu. Duk da rashin tsaro da yankin yake ciki, wasu yan siyasa na goyon bayan sakin wani na hannun Dan ta’adda Bello Turji da ake ci gaba da bincikenssa; inda suke goyon bayan ya kai kara kotu don neman a bashi hakkinsa na walwala.
Bayanan da Kungiyar ta samu daga kotu ya tabbatar da cewar wani mai aikin bayar da bayanai ga yan ta’addaya, wanda y kitsa da tabbatar da cewa yana hada baki, ya na goyon bayan yin aikin bayar da bayanai ga yan ta’adda a yankin na bukatar kotu ta wanke laifinsa don samun yanci.
Daga wannan batun na karar da aka kai kotu, ya zamo cewa akwai wadansu da suke ikirarin su manya kasa ne; ko yan boko ne masu ilimi tare da hadin guiwar wasu sannanun yan siyasa da hannu wajen yaduwar kai hare haren da ake yi duk da irin kokarin da Gwamnatocin jihohi da na tarayya ke aikatawa domin samun nasarar da kowa ke bukata wajen yaki da matsalar tsaro da nufin kakkabe yan bindiga da masu aikin ta’addanci da wadanda suke hada baki da su.
Dukiya da rayukan jama’a na kara shiga cikin hadari a kowace rana sakamakon matsalar kai hare hare da ake yi kuma duk da haka ana kokarin kawar da kai ana ta harkokin siyasa kawai ba tare da la’akari da wannan muhimman lamari ba da ke barazanar shafar mu baki daya har ma ya cinye mu.
Haka ma Kungiyar tana shawarta shugabannin gargajiya, shugabannin addini, shugabannin al’umma da su kara matsa kaimi wajen kara fadakar da jama’a da kuma a kodayaushe su taimakawa wadanda aka dorawa alhakin kare rayuka da dukiyar jama’a da muhimman bayanai da za su taimaka wajen cimma nasara.
A halin yanzu da watan Azumin Ramadana ke kara matsowa, muna kara roko da babbar murya ga Gwamnatin tarayya, Jihohi da sauran yan Najeriya da su taimakawa wadanda suka tsinci kansu cikin wannan halin har suka gudu daga gidajensu da garuruwansu musamman wadanda suke a sansanin masu gudun hijira suna neman agaji a sakamakon wannan matsalar ta rashin tsaro a cikin al’umma wanda hakan ya sa suke gudun tsira da rayukansu a yankin.