An sallami wani Dogari a masarautar Zazzau mai suna Sama’ila Abubakar Rimin Tsiwa daga aikinsa a masarautar da ke garin Zariya a jihar Kaduna, bisa zarginsa da yi wa wata mata fyaɗe a wata ziyarar aiki da takai fadar.
Abdullahi Aliyu Kwarbai, jami’in hulɗa da jama’a na masarautar a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, “An kori Dogarin mai suna Sama’ila Abubakar Rimin Tsiwa, daga aikin Majalisar Masarautar Zazzau bisa laifin yiwa wata mata fyaɗe.
Sanarwar ta ce, mai gadin fadar ya yaudari matar da take shirin ɗaurin aure, ta kuma zo neman taimako daga wajen Sarkin ta hanyarsa, inda ya ce maimakon ya kai matar wurin Sarki, Mai martaba Ahmed Nuhu Bamalli, sai wanda ake zargin ya yaudare ta zuwa wurin da abokansa suka yi mata fyaɗe.
KU KUMA KARANTA:Kotu ta yankema mai koyan aiki hukuncin ɗaurin rai da rai, kan laifin yima jaririyar ubangidansa fyaɗe
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, majalisar ta umarci ‘yan sanda da su gaggauta gudanar da bincike tare da tabbatar da an gurfanar da waɗanda suka aikata laifin ba tare da ɓata lokaci ba domin fuskantar fushin doka.
Majalisar Masarautar ta yi alkawarin bin diddigin lamarin domin ganin an yi wa matar adalci, a kwanan baya ma an kama wani mai rike da muƙamin da ke aiki a fadar tare da tsare shi a lokacin da ya yi wa wani ƙaramin yaro fyaɗe da ya je fadar a wata hanya, wannan mummunan lamari shi ne, ya haifar da firgici a Zariya.
[…] KU KUMA KARANTA: An kori Dogarin Masarautar Zazzau da ake zargi da yiwa wata mace fyaɗe […]