Labarin yana gefen ku!

Malaman firamare a Abuja sun gudanar da zanga-zanga, kan rashin biyan haƙƙinsu na albashi

1

Daga Maryam Umar Abdullahi

A ranar Talatar nan ne, malaman firamare a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, suka gudanar da zanga-zanga a dandalin “Unity Fountain” da ke birnin.
A yayin zanga-zangar, malaman sun zargi ƙananan hukumomin Abuja da yin wasarere da batun jin dadi da walwalarsu.

Malaman sun gudanar da zanga-zangar ne akan rashin biyansu bashin da suke bi na kuɗaɗen albashi da na ƙarin girma da kuma na mafi ƙarancin albashi tun daga shekarar 2019.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Filato ta sanya dokar hana fita na tsawon awa 24 a Mangu

Malaman sun buƙaci Ministan Abuja, Nyesom wike da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu su sa baki a lamarin.

Haka kuma sun yi ƙira da a sake fasalta tsarin ilmin firamare a ƙasar, inda suka buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙwace ragamar gudanar da makarantun daga hannun ƙananan hukumomi.

Malaman firamaren birnin Abuja sun shafe fiye da mako guda suna yajin aiki amma har yanzu sun ce babu wani takamaiman martani daga hukumomin da al’amarin ya shafa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.