Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi ƙira ga shugabannin addini da su daina tsine wa Najeriya a tarukansu ko wa’azi.
Tinubu ya bayyana haka ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Alhamis, yayin buɗa-baki da malaman addinai da masu sarautun gargajiya.
“A ranar Laraba na halarci jana’izar sojoji 17 da aka kashe a Okuama, Jihar Delta. Na ga matansu masu ciki da yara ƙanana.
”Soyayyar al’umma tana hannunku. Ku yi wa kasarmu addu’a. Ku bai wa yaranmu ilimi da tarbiyya. Wa’azin da muke yi wa mutane a coci da masallatai suna da muhimmanci.
“Kada ku la’anci al’ummarku. Wannan ita ce ƙasarku; kar a yi Allah-wadai da ita a cikin wa’azi, kada ku zagi ƙasar nan. Shugabanci na nufin kawo sauyi.
“A ce wannan shugaban ba shi da kirki, wannan ba laifi ba ne. Amma ku bari sai zabe na gaba sai ku sauya shi, amma ku daina la’antar kasar nan. Kar ku zagi Najeriya. Wannan kyakkyawar kasa ce.”
KU KUMA KARANTA: Tinubu ya karrama sojojin da aka kashe a Delta
Shugaban ya nusar da su muhimmancin sauya akidun mutane, ta hanyar cusa musu kishin kasa da dora su a hanya mafi dacewa.
Tinubu, ya buƙaci shugabannin addinai da suka kasance masu adalci wajen sukar masu rike da mukaman siyasa.
A gefe guda kuma, Tinubu ya jadadda wa shugabannin aniyarsa ta magance ɗimbin matsalolin da ake fuskanta a ƙasar nan nan.
Taron buɗa-bakin ya samu halartar sarakunan gargajiya daga Arewaci da Kudancin Najeriya da kuma malaman addinin Musulunci da na Kirista.
Shugaban Tinubu ya kuma buƙaci shugabannin gargajiya da na addinai da su kulla alaƙa mai ƙarfi da gwamnati domin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da sauran laifuka a ƙasar nan.
Mahalarta taron sun yaba wa Tinubu kan salon mulkinsa da kuma yadda yake jajircewa wajen kawo wa Najeriya sauyi mai ɗorewa.