Majalisar Dattijai za ta cire hukumar kula da Injiniyoyi daga kasafin kuɗi na 2023

Majalisar Dattijai ta ce babu gudu babu ja da baya wajen cire hukumar kula da injiniyoyi ta ƙasa COREN daga kasafin kuɗin 2023, tare ƙin ba ta ko Kobo a cikin kasafin kuɗin shekara mai kamawa.

Dambarwar ta soma ne lokacin da kwamitin ayyuka da Sanata Adamu Aliero yake shugabanta ya buƙaci rajistara na hukumar, Ademola Bello, da ya yi bayanin yadda hukumar ta kashe kuɗin da aka ware mata a kasafin kuɗin da ya gabata na wannan shekara ta 2022.

Kamar yadda rajistaran hukumar ya faɗa, an ware wa hukumar biliyan 2.4 a kasafin kuɗin wannan shekara ta 2022 kuma sun kashe biliyan 1.2 wajen shirya babban taron ƙungiyar na ƙasa.

Bello ya ce kuɗin ma’aikata ya ƙaru zuwa miliyan 200 a kasafin bana saboda COREN ta tsara cewa za ta buɗe ofisoshinta a jihohi 36 na ƙasar nan a 2023.

Da yake amsa tambayar shugaban kwamitin, Sanata Adamu Aliero; Bello ya ce COREN ta sanya kuɗi Naira miliyan 45 ga asusun gwamnatin tarayya wanda shugaban kwamitin ya buƙaci su kawo takardar aikewa da kuɗin zuwa asusun gwamnati.

Ɗaya daga cikin mambobin kwamitin, Sanata George Sekibo, ya ce babu dalilin cigaba da sanya hukumar Injiniyoyin a kasafin kuɗin ƙasa duba da yadda gwamnati ba ta amfana da hukumar duk da kuɗin masu yawa da take sakawa kan hukumar a kasafin kuɗi.
Ya ce ta yaya za a ba ku kuɗi har biliyan 2.4 amma kuma ku dawo da miliyan 45 ga asusun gwamnati a matsayin kuɗin shiga?

Ya ce ya kamata COREN ta tsaya da ƙafarta, kamar yadda ƙungiyoyin ƙwararru irin su ƙungiyar lauyoyi da ta likitoci da sauransu suka tsaya da ƙafarsu ba tare da sanya su cikin kasafin kuɗin ƙasa ba.

a ƙarshe dai kwamitin Sanata Adamu Aliero na ayyuka ya buƙaci COREN da su je su kawo takardun da ke nuna suna sanya kuɗaɗe ga asusun tarayya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *