An gano gawar ‘yar kasuwar da yan fashin suka kashe a Legas

1
374

Wata ‘yar kasuwa a Legas da ke zaune a yankin Ibafo da ke ƙaramar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun, Rosemary Obidinma, wacce iyalinta suka sanar da ɓatanta an gano ta, a mace.

An wayi gari da neman matar wacce mahaifiya ce ga ‘ya’ya biyar, ta tafi shagonta da ke Apapa a Legas bayan da taso daga shagon nata da take kasuwanci ba ta koma gida ba a ranar 2 ga watan Nuwamba.

Rahotanni sun nuna cewa ɗanta Daniel ya yi magana da ita ta ƙarshe da misalin ƙarfe 10 na dare, bayan haka da Daniel da ‘yan uwansa sun kira wayarta, sai wani mutum da ya ɗauki wayar ya gargade su da su daina tada masa hankali, yana mai cewa yana jihar Delta.

Daniel ya ce jami’in ‘yan sanda reshen ofishin Ketu, inda aka samu rahoton tun farko, ya kira shi tare kawunsa, Emmanuel Iffi a ranar Juma’a domin su zo su duba gawar mace da aka samu wacce ‘yan fashi da ake kira ‘yan ‘one chance’ suka kashe.

Damadai fashin one chance ya shahara a Legas, inda ’yan daban ke tuƙa motocin haya, sukan cika motar da ’yan ƙungiyarsu, wadanda ke yi kamar fasinja ne, domin su zalunci jama’a.

Daniel ya ce, DPO ya ce ‘yan sanda sun yi ta ƙoƙarin gano ‘yan uwan ​​gawar ba tare da samun nasara ba, “kuma a lokacin da ya nuna mana hoton gawar, sai naga mahaifiyata ce.

“Mun samu labari daga ’yan sanda cewa wasu ‘yan fashi ne da suka bindige ta suka caka mata wuka har ta mutu.

“Har yanzu gawar ta na nan a ɗakin ajiyar gawa, amma zuwa ranar Talatar wannan makon, za mu ɗauki gawar zuwa ƙauyenmu domin binne ta.”

1 COMMENT

Leave a Reply