Mahara sunyi awon gaba da miji da mata mai juna biyu a garin Illela, jahar Sakkwato

0
200

Wata majiya data zabi a boye sunanta ta bayyana maharan sun dira gidansa ne karfe 1:30 na dare, inda suka yi garkuwa da shi.

Wani mazaunin yankin ya ce “Sun shigo cikin Illela ne inda suka dirfafi wata unguwa da ake kira Kara, nan suka dauki wani mutum mai suna Friday shi da matar sa.

Saidai majiyar ta ƙara da cewa, bisani  matar ta kubuta basu yi nasarar tafiya da ita ba, sakamakon ganinta dauke da tsohon ciki.

Rahotonni sun jiyo cewa gugun ‘yan bindigan sun kai kimanin mutum 8 ko wannen su dauke da muggan makami. 

Leave a Reply