Connect with us

Labarai

‘Magoya bayan Lawan sun jefi gwamnan Yobe’

Published

on

Ana zargin wasu magoya bayan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da hargitsa tare da jifan Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, a wani taron murnar hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ta bayyana Lawan a matsayin ɗan takarar sanata na jam’iyyar APC mai mulki a Yobe ta Arewa a zaɓen majalisar dokokin ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa taron wanda ya samu halartar ɗaruruwan magoya bayan jam’iyyar APC, ya ninka na yaƙin neman zaɓen APC na yankin Yobe ta Arewa.

Gwamna Buni ya miƙe domin gabatar da jawabinsa, inda fusatattun magoya bayan da suka yi wa Lawan da babbar murya murna suka fara rera taken kin amincewa; ‘bamayi bamayi bamaso” – ma’ana “ba mu son ku”.

Magoya bayan da suka fusata daga bisani suka fara jifan gwamnan da sauran bakin da ke wurin taron, lamarin da ya tilasta wa taron yin katsalandan.

KU KUMA KARANTA: An kai wa tawagar Atiku Abubakar hari a Maiduguri

A cewar Premium Times, magoya bayan Lawan sun kai wa gwamnan hari ne saboda ana kyautata zaton ya goyi bayan abokin hamayyar Lawan, Bashir Machina, wanda shi ne ɗan takarar APC har sai da kotun ƙoli ta yanke hukuncin.

Idan ba a manta ba a ranar Litinin ɗin da ta gabata ne kotun koli ta ayyana shugaban majalisar dattawan a matsayin ɗan takarar sanata na jam’iyyar APC a jihar Yobe.

APC ta shigar da ƙarar Bashir Machina a gaban kotun koli inda ta yi ikirarin cewa Lawan ne ɗan takarar Sanatan Yobe ta Arewa a zaben 2023 mai zuwa.

Lauyan jam’iyyar, Sepiribo Peters a zaman da aka yi na karshe ya ce zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayun bara wanda ya haifar da Machina ya saba wa dokar zabe ta 2022.

Peters ya kara da cewa Danjuma Manga da ya gudanar da zaben fidda gwani wanda ya samar da Machina ba shi ne kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar ya gabatar da shi ba.

Sai dai lauyan Machina, Sarafa Yusuf ya yi addu’a ga Kotun Koli da ta yi watsi da karar da aka shigar kan rashin cancantar a bisa dalilin cewa Shugaban Majalisar Dattawa bai kalubalanci kararrakin ba a kotuna da kuma kananan kotuna.

Ya kuma yi nuni da cewa Manga wanda ya gudanar da zaɓen fidda gwanin inda Machina ya fito, mamba ne a kwamitin da aka nada na NWC domin gudanar da aikin.

Sai dai mai shari’a Centus Nweze, a wani hukunci da ta yanke a ranar Litinin, ya nuna rashin gamsuwa da yadda Machina ya shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta hanyar samo sammaci ba tare da shaidar baka da ke tabbatar da zargin damfara ba.

Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Sanata Ahmad Lawan ya musanta ɓarkewar rikici a taron APC na Yobe | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Jirgin Max Air ya tsallake rijiya da baya sakamakon fashewar tayoyi a Yola

Published

on

Jirgin Max Air ya tsallake rijiya da baya sakamakon fashewar tayoyi a Yola

Jirgin Max Air ya tsallake rijiya da baya sakamakon fashewar tayoyi a Yola

Daga Idris Umar, Zariya

Wani Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Max Air NGL1649, Boeing 737 mai lamba 5N-ADB ya tsallake rijiya da baya a jiya Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa Jirgin wanda ke ɗauke da fasinjoji 119 da ma’aikatan jirgi 6 yana tsaka da shirin tashi daga filin jirgin sama na Yola jihar Adamawa inda zai nufi Abuja sai kwatsam aka ji duka tayoyin jirgin guda huɗu sun yi bindiga sun fashe lamarin da ya jawo dole aka fasa tafiyar aka sauke fasinjojin.

KU KUMA KARANTA: Jirgi ya yi saukar gaggawa bayan fasinja ya gartsa wa ma’aikaciya cizo

Rahotanni sun nuna cewar karfe 7 na safe ya kamata matafiyan su tashi amma sakamakon Fashewar waɗannan tayoyi sai karfe biyu na dare sannan suka sami damar ɗagawarsu.

Continue Reading

Labarai

Ɗangote ya janye aniyarsa ta shiga kasuwancin sarrafa ƙarafa

Published

on

Ɗangote ya janye aniyarsa ta shiga kasuwancin sarrafa ƙarafa

Ɗangote ya janye aniyarsa ta shiga kasuwancin sarrafa ƙarafa

Shugaban kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Dangote ya sanar da janye aniyarsa ta shiga kasuwancin ƙarfe a Najeriya.

Janyewar da hamshaƙin ɗan kasuwar ya yi na zuwa ne watanni biyu bayan kamfaninsa ya sanar da cewa zai zuba jari a ɓangaren sarrafa ƙarafa domin faɗaɗa tattalin arziƙin Najeriya.

A yayin da yake jawabi ga manema labarai a Legas a ranar Asabar, shahararren mai kuɗin ya bayyana cewa kamfanin nasa ya janye daga wannan kasuwancin ne domin kada a zo ana zargin kamfaninsa da babakere.

Fitaccen ɗan kasuwar ya kuma yi watsi da zargin da ake yi wa wasu kamfanoninsa na babakere a harkokin kasuwanci.

“Kun san kan batun sabon kasuwancin da muka sanar, wanda shi ne na ƙarafa, a gaskiya kamfaninmu ya yanke shawarar cewa ba za mu yi kasuwancin ƙarfe ba domin idan muka yi kasuwancin, za a rinƙa ƙiranmu da sunaye iri-iri kamar masu babakere,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Matatar Ɗangote na zargin manyan kamfanonin mai na duniya da hana shi samun ɗanyen fetur

“Haka kuma za a bayar da ƙwarin gwiwar shigo da kayayyaki, ba za mu so mu shiga nan ba.”

“Idan kuka dubi duka ayyukanmu a Ɗangote (Group), muna ƙara ƙima; mukan dauki kayayyaki wanda aka samar da su a cikin ƙasa mu sarrafa su zuwa kayayyakin amfani, mu kuma sayar.

Ba mu taba hana kowa a sane ko cikin rashin sani ba daga yin irin kasuwancin da muke yi. “Lokacin da muka fara kasuwancin siminti, Lafarge ne kawai ke aiki a nan Najeriya.

Babu wanda ya taba ƙiran Lafarge a matsayin mai babakere,” in ji shi. Shugaban kamfanin na Ɗangote ya bayyana cewa ƙiran kamfaninsa da ake yi da mai babakere ba ya yi masa daɗi a ransa.

Continue Reading

Labarai

Najeriya na tunkarar wani mataki mai haɗari saboda wahalhalun tattalin arziki – CNG

Published

on

Najeriya na tunkarar wani mataki mai haɗari saboda wahalhalun tattalin arziki - CNG

 

Najeriya na tunkarar wani mataki mai haɗari saboda wahalhalun tattalin arziki – CNG

Gamayyar ƙungiyoyin arewacin Najeriya, CNG,
ta ce ba a taɓa samun gwamantin da aka sami koma-baya ba a Najeriya, kamar mulkin Bola Ahmed Tinubu ba.

A cewar CNG, maimakon a samu ci gaba sai ma koma-baya a ake ta samu, saboda manufofin da gwamantin ta ke futo da su babu wanda zai ce tana jin ƙasan talakan ƙasar.

Kwamared Jamilu Aliyu Chiranci shi ne shugaban ƙungiyar ta CNG, ya shaida wa BBC cewar Najeriya na tunkarar wani mataki mai haɗari, saboda wahalhalun tattalin arziki, da hauhawar farashi, da talauci da ya yi wa ƴan ƙasar katutu

KU KUMA KARANTA:Da ba a cire tallafin mai ba, da wahalar da za’a sha a Najeriya ta fi ta yanzu – Gwamnatin tarayya

Ya ce dole CNG ta sa daukar wannan mataki sakamakon yadda ake ci gaba da fuskantar matsin rayuwa musaman tashin farashin kayayyaki a ɗaukacin faɗin ƙasar.

Gamayar ƙungiyoyin arewacin ta Najeriya ta ce, lamarin ƙangin da ake fama da shi a ƙasar ya fi ƙamari a yankin arewacin ƙasar, saboda yanayin da al’ummar yankin ke ciki.

Duk abinda shugaban ƙasa zai yi, akwai buƙatar ya tsaya ya mayar da hankali kan ceto ƙasar nan, wanda ina da yaƙinin cewar bazai so a ce a lokacin sa Najeriya ta shiga yanayin da ƴan ƙasar za su yi mata turjiya ba”

Sannan ya ce ’mutam miliyan 133 a Najeriya na fama da talauci, sannan mutane miliyan 20 ba su da aikin yi ko ma a ce ba su da isasshen aiki”, In ji Kwamrated Chiranci.

Da hakane CNG ɗin ta bai wa shugaban ƙasar Ahmed Bola Tinubu wa’adin mako guda da ya hanzarta tare da yin nazari game da halin da al’ummar ƙasar ke ciki, tare da ɗaukar matakan gaggawa da za su kawo wa ƴan Najeriyar sauƙin rayuwa.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like