Kuyi min addu’a aurena na 6 na ƙoƙarin rugujewa-Adam A. Zango

2
578

Adam A. Zango, fitaccen furodusa kuma jarumi a masana’artar fim ta Kannywood wanda aka haifa a ranar 1 ga Oktoba, 1985 a unguwar Zango ta jihar Kaduna, iyayensa su ne Abdulahi Zango da Yelwa Abdullahi, bayan makarantar Islamiyya, Zango bai ci gaba da karatunsa ba sai dai ya koma Kano a matsayin ɗan rawa, kuma mawaƙi.

Adam a lokacin da ya ke sana’ar sa ya samu nasara har ya tafi da zuciyar fitattun jarumai mata a masana’antar Kannywood tare da alkawarin zai aure su, amma sai ya barsu, yaje ya auri wasu.Fitattun matan sun haɗa da Nafisa Abdullahi, Maryam Booth, Zainab Indomie, da dai sauransu. Akwai Fati AB Yola wadda ya aura amma daga baya ya rabu da ita, tun daga nan ake kiransa da mayaudari, ko kuma mai auri saki, ma’ana kullum yana aure kuma yana sakin aure.

KU KUMA KARANTA: Adam A Zango, jarumin mu na wannan makon

Lokacin da ya kori matarsa ​​ta 5 zai auri Safiya Chalawa daga jihar Kebbi, iyayenta sun nemi yayi alqawari cewa ba zai taɓa sakin ɗiyarsu ba wanda ya amince, kuma aka ɗaura auren, yanzu sun haifi ɗiya mace kyakkyawa, gaba ɗaya Adam Zango yana da ‘ya’ya 6 duk daga uwaye 6 daban-daban.

A jiya ya fitar da wani faifan bidiyo a dandalin sada zumunta yana bayyana ɓacin ransa kuma yayin da zai sake rabuwa da matarsa ta 6,​​Safiya Chalawa. “Na bude mata kasuwanci a kafafen sada zumunta, kuma tana samun kuɗi sosai, amma daga baya na gano cewa tana cikin ƙungiyoyi da dama da suka hada da ‘Uwar Adashe’, ma’ana yanzu ita ce shugabar wata ƙungiya da ake adashin kuɗi ba tare da izinina ba, tana kuma yaɗa hotunanta a dandalin sada zumunta ciki harda hotunan da babu cikekken sutura.

Na dakatar da ita amma ta ƙi, a yanzu haka da nake magana bata gidana har na tsahon watanni uku.” Na tura yan uwana wajen yan uwa ta don su tattauna sharaɗina guda 3. Ɗaya, ta dena saka hotunanta a kafafen sada zumunta, na biyu ta bani wayar dana bata domin in siyo mata wata, wacce bata da lambobin mutane, kuma daga ƙarshe zan chanza mata gidan da za ta zauna a ciki saboda ba ta jituwa da ‘yanuwana da yarana, amma ta ƙi amincewa da sharudɗan.

Shahararren jarumin na kannywood ya ƙara da cewa ya riga yayi mummunan suna a masana’antar amma yana yin wannan bayanin ne domin mutane su riƙa yi masa addu’a domin a duk lokacin da zai ɗauki mataki mai tsauri a kan matarsa ​​yana shiga cikin damuwa, tunanin mai mutane za suce sai yasa na kasa ɗaukan mataki.

Yanzu haka, ina tunanin ɗaukan hukunci dindindin, ba na alfahari da abin da ke faruwa a rayuwarsa, amma ba shi da wani zaɓi da ya wuce ya fito fili ya bayyana abin da ke faruwa game da iyalinsa.

A kwanakin baya ne dai fitattun jaruman kannywood da jaruman fina-finan Hausa suka yi aure, wanda ya haɗa da Halima Atete, Rukayya Dawaiyya, Hafsat Idris da Ummi Rahab da ta zauna a gidan Zango a baya a kan cewa za ta aure shi, amma ta auri Lilian Baba -Mawaƙin hip hop, lamarin da ya tayarwa da Adam Zango hankali, saboda soyayyar da yake mata.

2 COMMENTS

Leave a Reply