Kungiyar Haske Ta Tallafawa Marayu 764 Da Kayan Sallah

0
352

Daga; Isah Ahmed, Jos.

KUNGIYAR nan ta Haske da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato, da ke tallafawa marayu da gajiyayyu, ta tallafawa marayu maza da mata da gajiyayyu guda 764, da kayan Sallah. Shugabar Kungiyar, Hajiya Maryam Shehu Nabage ce, ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da wakilinmu.

Ta ce duk da yadda shekarar bana ta kasance na halin matsi, sun yi kokarin rabawa marayu da gajiyayyu guda 764, tufafin sallah a wurare daban daban na ciki da wajen Najeriya.

Ta ce wuraren da suka raba kayan, sun hada da nan Jos da jihohin Bauchi da Kano da Kaduna da Katsina da Jam’horiyar Nijar.

Ta ce kayan da suka raba, sun hada da yadudduka da shaddoji da Atamfofi da takalmin silifa kafa 220.

Hajiya Maryam ta yi bayanin cewa kan maganar ciyarwa kuwa, kamar yadda suka saba a duk lokacin Azumi, a bana ma kullum suna tuka tuwon shinkafa da tuwon masara suna rabawa marayu, tun farkon Azumi har karshen Azumin.

Ta yi kira ga masu hali, su taimaka masu kan wannan aiki da suka sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here