Ku Tabbatar Kun Zabi ‘Yan Takarar Da Suka Dace – Atiku Ga Wakilan PDP Kaduna

0
301

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON mataimakin Shugaban Kasar Najeriya kuma dan takarar Shugabancin Kasar a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya buƙaci masu zaben yan takara a Jihar Kaduna da su yi kokarin tabbatar da sun zabi Jajirtattun mutane wadanda zasu tsayar takara a zaben fidda gwani na Jam’iyyar da zai gudana.

Dan takarar Atiku Abubakar, ya bayyana hakan ne a garin Kaduna a ranar talata yayin ganawa da wakilan Jam’iyyar PDP masu zaben yan takarar Jam’iyyar, inda ya furta cewa yana da yakinin Jam’iyyar ce ta yi nasara a zaben shekarar 2015 da 2019 a Jihar da kasar baki daya.

Ya kara da cewa Jihar Kaduna gida ne a gare shi kuma a yanzu ya zo gida ne domin ganawa da yan uwan shi kuma ya nemi goyon bayan ‘ya’yan Jam’iyyar tare da wakilan domin tabbatar da tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa a tutar Jam’iyyar.

Ya ce ” a PDP na ci zabe a shekarar 2019 amma aka kwace mana har da nan Jihar Kaduna, amma wannan karon muna son ku kare, ku tsare don haka yasa muka sake dawowa neman goyon bayan ku na sake tsayawa takara a wannan karon.”

“Na dauki alkawarin maganin wannan bala’in da Jam’iyyar APC ta kawo mana na talauci, rashin tsaro, rashin aikin yi da yunwa, don haka mun dauki alkawarin dawo muku da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali idan kuka zabe mu.”

“Wadannan na daga cikin kudirori biyar da nayi alkawarin kamar yadda na fada a garin Abuja, sannan zan zauna da yan Majalisu, Gwamnoni da Wakilanmu domin tabbatar da an shirya tsare-tsaren ba kananan hukumomi yancinsu, kana da warware matsalar Kungiyar malaman Jami’o’i.”

Tsohon mataimakin Shugaban Kasar, kuma Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar ya jinjinawa al’ummar Jihar ta Kaduna da wakilan Jam’iyyar bisa kokarin da suke na ganin cewa sun tsayar da yan takarar nagari a zaben fidda gwani da za a gudanar nan da wasu yan kwanaki.

Da yake jawabi a madadin Dattawan Jam’iyyar, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, kuma tsohon Shugaban riko na Jam’iyyar, Sanata Ahmad Makarfi, ya ce dan takarar haziki ne wanda ya cancanci zama Shugaban Kasar Najeriya don haka basa shakka a kan burinsa.

Ya kara da cewa ya zame masu wajibi su zo su tare shi jin cewa zai zo domin Jihar Kaduna garin ne wanda hakan ya sanya barin garin Abuja domin zuwa ya tarbe shi da tsohon Gwamnan Jihar Muktar Ramalan Yero, tare da tsohon Sanatan Shiyyar Kaduna ta tsakiya Kwamared Shehu Sani.

Hakazalika da jake jawabin maraba ga Dan takarar, Shugaban Jam’iyyar PDP ta Jihar Kaduna, Honarabul Hassan Hyet, ya bayyana cewa wannan wani nauyi ne ya rataya a wuyansu na ganin cewa sun tabbatar da ba shi goyon bayan domin shi cikakken dan Jihar Kaduna, illa Jihar Adamawa Kasar shi ce ta haihu kawai.

Shugaban Jam’iyyar, ya yiwa Dan takarar fatan alheri na samun nasara tare da yin alkawarin Kokarin ganin duk wakilan Jam’iyyar sun zabe shi a zaben fidda gwani na Jam’iyyar.

Leave a Reply