Kaduna 2023: Ni Ne Mafi Cancantar Zama Dan Takarar Gwamna A PDP – Ramalan Yero

0
321

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON Gwamnan Jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, a ranar Juma’a ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi kowa kwarewa da kwarin guiwa wajen neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) gabanin zaben 2023 a Jihar.

Tsohon gwamnan wanda ya kasance a sakatariyar jam’iyyar a ranar Juma’a 20 ga watan Mayu, 2022, ya shaida wa shugabannin jam’iyyar PDP da masu son tsayawa takara su tuna da tarihin siyasarsa da abin da ya iya yi a lokacin da ya yi wa jihar hidima a wurare daban-daban, inda ya bukace su fara yin la’akari da shi a lokacin zaben fidda gwani da za a yi a jihar.

Ya ce “idan aka yi la’akari da irin abubuwan da ya faru a baya da kuma kokarin da na yi a matsayinna na tsohon ma’aikacin gidan Sir Ibrahim Kashim da kuma sabbin ilimin da ya karawa a cikin shekaru bakwai da suka wuce, zai iya magance tattalin arziki, lafiya, ilimi, kawo hadin kai, jin dadin ‘yan kasa da kawar da sauran kalubalen da ke kawo cikas a jihar idan aka sake ba shi dama.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan ziyarar da suka kai a sakatariyar jam’iyyar, kwararren masani kan harkokin kudi ya ce, “a yau mun samu damar ziyartar ofishin babbar jam’iyyar mu da ke cikin babban birninmu na Kaduna, domin mu kara kusantar shugabanni da masu kishin kasa kan burinmu na niyyar tsayawa takarar gwamna a karkashin jam’iyyar.

“Na shaida musu cewa ni gwamna ne a baya kuma na yi wa jihar hidima a wurare daban-daban wanda hakan ke nufin ni ba bako bane a jam’iyyar da jama’armu a jihar.

“Saboda halin da muka tsinci kanmu a yau da kuma kasa baki daya kamar kalubalen tsaro, tattalin arziki, ilimi, lafiya, hadin kai da jin dadin jama’a, sai muka ji cewa wasu daga cikinmu da suke can a da kuma suna iya yin aikin sun ga bukatar hakan domin mu zo mu magance wadannan kalubale domin mu samu kwanciyar hankali da wadata.

“Don haka na zo ne domin in sanar da jam’iyyar cewa ina cikin takara sannan in yi kira ga shugabannin jam’iyyar da wakilan jam’iyyar su duba abin da muka yi da abin da za mu iya yi idan aka ba mu dama”. Ya ce.

Leave a Reply