Kafa Kwamitin Sasantawa Zai Kawo Ci Gaban Jam’iyyar APC A Kano – Usman Dan-Gwari

0
286

JABIRU A HASSAN,Daga Kano.

SHUGABAN Kwamitin riko na kungiyar masu sana’ar kayan gwari Alhaji Usman B. Dan gwari ya ce idan aka kafa kwamitin sasantawa ko shakka babu Jam’iyyar APC za ta sami maslaha da daidaito a Jihar Kano da Kuma kasa baki daya.

Ya yi wannan tsokaci ne a zantawar su da manema labarai a Zariya, inda ya jaddada cewa duk da rikicin cikin gida da Jam’iyyar ta APC ke ciki a wasu Jihohin wannan kasa, Jam’iyyar tana da karfin da zata lashe zabukan shekara ta 2023 da za a gudanar nan gaba kadan cikin yardar Allah.

Usman B. Dangwari, ya Kara da cewa idan jam’iyya tana da magoya baya masu tarin yawa, dole ne a sami rigingimun cikin gida tattare da ita, amma idan aka kafa kwamitin sasantawa ko shakka babu kwalliya za ta biya kudin sabulu wajen samun maslaha mai kyau.

Sannan ya bayyana cewa a shirye suke wajen yin aiki tukuru ta yadda kasarnan za ta ci gaba da samun ci gaba a tsari irin na dimokuradiyya, tare da bunkasa tattalin arziki da kuma samun zaman lafiya mai dorewa tsakanin sassan kasa kamar yadda abubuwa suke tafiya a zamanin baya.

Ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga matasan Jihar Kano da Kuma na sauran bangarorin kasarnan da su kasance masu bin doka da son zaman lafiya a lokutan yakin neman zabe musamman ganin cewa sune ake gani a sahun gaba wajen kawo sauyi a shugabanci.

A karshe, Alhaji Usman Dan-Gwari, ya yi fatan alheri ga daukacin al’ummar Jihar Kano da Najeriya musamman masu sana’ar gwari wadanda suke a Kan gaba wajen samar da aiyukan dogaro da kai da kuma hada Kan al’umma.

Leave a Reply