Kaduna: Uba Sani Ya Doke Wasu Mutane 2 Da Suka Yi Takarar Neman Tiketin Kujerar Gwamna A APC

0
328

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

DAN majalisa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a zauren majalisar dattawa, Sanata Uba Sani ya lashe Zaben fidda gwani domin zama dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Kaduna.

Sanata Uba Sani, ya doke wasu ‘yan takara biyu ne a fafatawar da suka yi yayin gudanar da zaben fidda gwani na Jam’iyyar a dandalin murtala dake Kaduna a daren ranar Alhamis inda ya yi nasara.

Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na tsayar da dan takarar gwamnan APC na Kaduna, Anachuna Izu, a lokacin da yake bayyana sakamakon, ya ce Sanata Sani ya samu kuri’u 1,149 inda ya samu tikitin takarar gwamna, yayin da wanda ya zo na biyu, Bashir Abubakar ya samu kuri’u 37. Sani Sha’aban ya samu kuri’u 10 inda ya zo na uku.

Wakilai 1,245 ne aka amince da su don kada Kuri’un, yayin da Jimillar kuri’un da aka kada sun kai 1,235 wanda daga cikin kuri’un 1,196 da aka kada, kuri’u 39 ba su da inganci.

A jawabinsa na godiya, sanata Sani ya bayyana fitowar sa a matsayin nasara ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC da daukacin al’ummar jihar Kaduna.

Ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kan ayyukan da Gwamna Nasir El-Rufai ya dora idan har ya zama Gwamnan Jihar bayan zaben 2023.

Hakazalika, ya buƙaci sauran masu son tsayawa takara, da su hada kai da shi a kokarinsa na ganin jihar Kaduna ta samu ci gaba.

Ya ce, “Saboda haka, ina mika godiyata ga abokan takarara, Alhaji Mohammed Sani Sha’aban da Alhaji Bashir Abubakar bisa yadda suka amince da tsarin dimokradiyya.

“Zan tuntubi wadannan manyan ‘yan siyasa da dabaru, in mika musu hannu na zumunci. Zan yi matukar godiya idan za su iya hada hannu da ni don kai jihar Kaduna zuwa ga tudun mun tsira.

“Wannan ita ce nasarar ku. Wannan shi ne lokacin ku. Wannan shi ne farkon tafiya na ƙarfafawa da ci gaba. Zamu dora a kan kyawawan abubuwan da shugabanmu, Gwamna Nasir El-Rufa’i ya yi don dorawa daga inda ya tsaya. Tare za mu tinkari kalubalen mu, mu samar da hadin kai a tsakanin jama’armu.

Zaben fidda gwanin takarar gwamna wani shiri ne na baje kolin tsari, nuna ladabi, hakuri da da’a daga wakilai. Mun nuna cewa mun yi imani da tsarin dimokuradiyya kuma a shirye muke mu bi bin doka da oda. Dimokuradiyya shi ne game da shiga.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here