Jihar Yobe a shekaru 33, wane irin ci gaba aka samu?

0
75
Jihar Yobe a shekaru 33, wane irin ci gaba aka samu?

Jihar Yobe a shekaru 33, wane irin ci gaba aka samu?

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jihar Yobe tana ɗaya daga cikin jihohi guda Tara (9) da tsohon shugaban ƙasa Janaral Ibrahim Badamasi Babangida ya ƙirƙiro a ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 1991. Jihohin sune; Abia, Enugu, Delta, Jigawa, Kebbi, Osun, Kogi, Taraba da Yobe. Ƙarin jihohi 9 da IBB ya yi a shekarar 1991, shi ne ya mayar da jihohin Nijeriya 30 cif-cif.

A shekarar 1996, Janaral Sani Abacha ya ƙara jihohi guda Shida (6). Sune Ebonyi, Bayelsa, Nasarawa, Zamfara, Ekiti da Gombe. Shi ne ya mayar da jihohin Nijeriya 36.

Jihar Yobe tana da ƙananan hukumomi guda 17. Sune Damaturu, Potiskum, Bade, Machina, Jakusko, Fika, Fune, Nangere, Nguru, Gujba, Gulani, Yusufari, Yunusari, Tarmuwa, Gaidam, Bursari da Karasuwa.

A duk ranar 27 ga watan Agusta na kowace shekara ana tuna wa da wannan rana mai muhimmanci a Jihar Yobe.

Alhaji Sani Ahmad Daura shi ne gwamnan jihar Yobe na farko. Ya mulki jihar Yobe daga 1991 zuwa 1992. Ya sauka ne sakamakon zaɓe da aka yi a wannan shekarar.

Alhaji Bukar Abba Ibrahim shi ne ya lashe zaɓen a ƙarƙashin jam’iyar SDP. Ya mulki jihar ne daga Janairun shekarar 1992 zuwa Nuwamban shekarar 1993. Ya sauka ne sakamakon rushe zaɓen da aka yi a duk faɗin ƙasar.

Com-Pol Dabo Aliyu shi ne gwamnan jihar Yobe na uku, daga 1993 zuwa 1996. Wing Commander John Ben Kalio shi ne gwamnan jihar Yobe na Huɗu. Ya mulki jihar Yobe daga 1996 zuwa 1998.

Kanal Musa Muhammad shi ne gwamnan jihar Yobe na Biyar. Ya mulki jihar Yobe ne daga 1998 zuwa 1999. Yana kan mulki aka yi zaɓen Dimokraɗiyya na shekarar 1999.

Alhaji Bukar Abba Ibrahim ne ya sake lashe zaɓen a ƙarƙashin jam’iyar APP. Ya yi shekaru 8 yana mulkin jihar Yobe.

An sake zaɓe a shekarar 2007, wanda marigayi Sanata Mamman B. Ali ya lashe zaɓen a ƙarƙashin jam’iyar ANPP. Sanata Mamman B. Ali shekaru biyu ya yi yana mulkin jihar Yobe, sai Allah ya masa rasuwa.

Ya rasu yana kan kujerar gwamnan. Rasuwarsa ne yasa aka rantsar da mataimakinsa, Alhaji Ibrahim Gaidam a matsayin sabon gwamnan jihar Yobe.

KU KUMA KARANTA: Matashi ya koma rayuwa a cikin kogon bishiya a Yobe

Alhaji Ibrahim Gaidam, shekaru 10 ya yi yana mulkin jihar Yobe. Ya ƙarasa shekaru biyu na Marigayi Sanata Mamman B. Ali, sannan an sake zaɓen shi a karo biyu. Wato 2011 da 2015. Ya kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2019.
Alhaji Mai Mala Buni shi ne ya gaje shi. Ya lashe zaɓe a shekarar 2019. An sake zaɓensa a shekarar 2023. Shi ne gwamnan Yobe zuwa yanzu. Ya lashe zaɓen ne ƙarƙashin jam’iyar APC.
A shekaru 33 jihar Yobe ta yi gwamnoni 8 kenan.

A waɗannan shekaru 33, waɗanne nasarori aka samu, sannan a wane wuri aka gaza.
Idan za a duba yadda siyasa ta kasance a jihar Yobe tun dawowar Dimokraɗiyya a shekarar 1999, za a iya cewa an fafata sosai daga 1999 zuwa 2007. Amma daga shekarar 2007 siyasar adawa ta yi sanyi sosai a jihar Yobe. A Yobe ta Kudu (Zone B) ne kaɗai ake siyasa mai zafi har yanzu. Wadda ake fafata wa tsakanin jam’iyyu. Amma a sauran sassan jihar Yobe kam, jam’iya mai mulki ce take lashe kusan dukkan kujerun da ake zaɓen. In ban da zaɓen 2019 wanda ɗan majalisar jiha mai wakiltar Nguru ya lashe zaɓen a ƙarƙashin jam’iyar PDP, shi ma daga baya ya koma jam’iyar APC mai mulkin jihar.

GYARAN HANYOYI DA MAGUDANAN RUWA
Babu shakka an yi hanyoyi, kwaltuna da magudanan ruwa (kwalbati) a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar Yobe, musamman babban birnin jihar, wato Damaturu. Garin Damaturu ya samu gyara sosai. Sai dai akwai gyara ko gyare-gyare sosai a sauran ƙananan hukumomin jihar. Ana fama da matsaloli, musamman rashin magudanan ruwa (kwalbati), wanda hakan yake janyo ambaliyar ruwa, lokaci bayan lokaci da sanadiyyar rushewar gidajen jama’a.

Ko a shekaru biyu da suka gabata an samu ambaliyar ruwa a garin Ngelzerma dake ƙaramar hukumar Fune. Ga shi kuma a wannan shekarar ma ta faru a garin Potiskum. Garuruwa da dama a jihar Yobe suna fama da rashin magudanan ruwa. Jama’a suna shiga matsanancin tashin hankali da Damina (idan ruwan sama ya fara sauƙa).

RAYA KARKARA
Babu shakka wasu daga cikin gwamnonin sun yi ƙoƙari wajen yin hanyoyi ga al’ummar da suke ƙauyuka domin sauƙaƙa musu zirga-zirga zuwa birane da kuma samun sauƙin tafiya Gona. Sannan ƙauyuka da dama an tona musu Borehole domin sauƙin samun ruwan da za su sha har su ba wa dabbobinsu. Amma al’ummar wasu ƙauyukan suna koka wa matuƙa a kan yadda aka mance dasu gabaɗaya a batun raya karkara. Misali kamar hanyar Jajere zuwa Potiskum. Da kuma wasu da dama waɗanda ba sai an ambata don gudun tsawaita wa. An mance dasu a batun gyara, amma idan zaɓe ya ƙarato ana tuna wa dasu, domin neman ƙuri’arsu.

HARKAR NOMA
Gwamnatin jihar Yobe tana raba Takin zamani, sannan tana sauƙaƙa farashinsa domin Talakawa su samu damar saya. Amma manoman suna koka wa da ba a ba su, wasu shafaffu da mai ne suke handamewa. Amma duk da haka ana Noma sosai a jihar Yobe, kuma babu abin da ba a Noma wa. Sai dai akwai buƙatar gwamnatin jihar ta tallafa wa manoma. Don da a ce ana ba su takin zamanin, noman da za a yi yana da yawan gaske.

HARKAR ILIMI
A ɓangaren ilimi kam za a iya cewa sam barka ta wani wajen! Domin kuwa an inganta wasu makarantu tun daga Firamare har zuwa jami’a. Sannan tun dawowar Dimokraɗiyya a shekarar 1999, ɗalibai ba sa biyan kuɗin rubuta jarabawar kammala Sakandire a makarantun gwamnati. Sannan kusan dukkan makarantun firamare da Sakandire an kewaye su. Sai dai akwai ƙorafin rashin isassun Bencinan zama a wasu makarantun da kuma rashin isassun takardun karatu a Library.

Wasu makarantun an yi gine-gine masu kyau har da Benaye. Sai dai akwai buƙatar a ɗebi Malamai masu koyarwa, musamman masu shaidar karatun Digiri, NCE da sauransu. Sannan an gina katafariyar jami’a mallakin jihar Yobe, wanda ɗalibai daga ko ina a faɗin ƙasar nan suna karatu a cikin ta. Sannan akwai jami’ar Gwamnatin Tarayya dake garin Gashuwa. Ita ma tana nan tana ta bunƙasa da ɗimbim ɗalibai a cikin ta.

Sai dai fa wasu makarantun gwamnatin jihar ta manta dasu a ɓangaren gyaran, misali irin makarantar Sakandire ta Fika GSS Potiskum da sauransu. Wannan makarantar tana buƙatar gyara ne gabaɗaya, domin kusan dukkan gine ginen makarantar ya tsatstsage wani ɓangaren ma ya rushe.

HARKAR LAFIYA
A Harkar lafiya an samu ci gaba sosai. An raya Asibitocin Karkara. Ƙauyukan da basu da Asibitoci, an je an gina musu Asibitin Kar-Ta-Kwana, domin agajin gaggawa. An inganta manyan Asibitocin ƙananan hukumomi (General Hospitals) an musu gine-gine masu kyau na zamani. An kawo kayayyakin aiki masu inganci. Yanzu saura a kawo ƙwararrun likitoci a kowane ɓangaren. Wasu ma an mayar dasu Specialist.

An gina katafaren Asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Yobe (Yobe State University Teaching Hospital) a birnin Damaturu. Asibitin zai iya zama na biyu ko na uku a Arewacin Nijeriya. Akwai ƙwararrun likitoci a fannoni daban-daban dake aiki a Asibitin.

KASUWANCI
Harkar kasuwanci tana ta haɓaka a jihar Yobe, musamman garin Potiskum da yake nan ne cibiyar kasuwancin jihar. Yanzu haka sabuwar gwamnatin Alhaji Mai Mala Buni ta fara gina kasuwannin zamani a garuruwan Damaturu, Potiskum, Gashuwa da Nguru. Sannan ita dai wannan gwamnatin ta farfaɗo da kamfanin yin Fulawa (Yobe Flour Mills) dake garin Potiskum. Da kuma kamfanin yin kwanukan rufi da na Leda dake Damaturu. Duk an farfaɗo dasu sun fara aiki.

BIYAN ALBASHIN MA’AIKATA
Ma’aikata ba sa kuka a kan rashin biyansu albashi a jihar Yobe, daga wata ya kusa ƙarewa albashinsu yake shiga asusunsu na Banki. Lallai ana yaba wa gwamnatin jihar Yobe a kan wannan. Amma hakan asali ya ɗauko tun lokacin mulkin Alhaji Bukar Abba Ibrahim.
Sai dai kash! A watan da ya gabata an samu matsalar yankewar albashin ma’aikata, wanda hakan ya jefa da dama cikin matsala. Kuma gwamnatin jihar ba ta fito ta yi gamsashshen jawabi game faruwar hakan ba.

ƊAUKAR MA’AIKATA
Ɗaukar ma’aikata gaskiya kai tsaye za a iya cewa ba a yi, sai dai abin da ake kira replacement, shi ma sai ‘ya’yan masu riƙe da madafun ikon jihar ke samu. Ɗan talaka kam ko oho!

Yanzu abin da ya fi tayar da ƙura da cece a faɗin jihar Yobe, musamman soshiyal midiya shi ne rashin zaman gwamna Mai Mala Buni a cikin jihar. Wasu suna ganin ya ajiye muƙamin shugabancin jam’iyar APC ɗin, ya dawo jihar ya zauna kamar yadda kowane gwamna yake yi, domin kuwa Hausawa na cewa ‘Taura Biyu ba ta taunuwa’.

Mafi yawan ‘yan jihar suna ganin ya fi muhimmantar da aikin jam’iyar APC na ƙasa, a kan aikinsa na gwamna. Kuma lallai Biri ya yi kama da mutum. Domin Gwamna Mai Mala Buni, tun da aka zaɓe shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Yobe, bai taɓa zama na tsawon wata guda cur a cikin jihar Yobe ba.
Sai dai a tattaunawar da gwamnan ya yi da gidan Rediyon BBC, a shirinsu na ‘A Faɗa A Cika’ ya ba da amsa ga masu yi masa wannan tuhuma. Inda ya ce ” zamana a cikin jihar ake so ko kuma aiki? Kullum ina approved na file da yawa. Don haka aiki ake buƙata, kuma ana yi, ba wai zamana a jihar ba”

Allah ya haɗa kan al’ummar jihar Yobe, ya cire musu ƙabilanci, domin ciyar da jihar gaba.

Ibraheem El-Tafseer Potiskum
(eltafseer15@gmail.com)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here