Matashi ya koma rayuwa a cikin kogon bishiya a Yobe

0
169
Matashi ya koma rayuwa a cikin kogon bishiya a Yobe

Matashi ya koma rayuwa a cikin kogon bishiya a Yobe

Daga Ibraheem El-Tafseer 

Wani matashi mai suna Muhammadu mazaunin wani ƙauye kusa da ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe, ya haƙura da rayuwa cikin garinsu, ya koma rayuwa cikin kogon wata bishiyar Kuka, yau kimanin shekaru biyar yana rayuwa a cikinta, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Wakilin Neptune Prime Hausa ya tuntuɓi wani mazaunin garin Fika, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da labarin.

Inda ya ce Muhammadu ya shaida wa mazauna yankin cewa, dalilansa da suka saka ya koma rayuwa cikin kogon bishiyar Kuka shi ne, Allah ya yi masa wata baiwa ta sanin abubuwan da za su iya faruwa cikin kwanaki ko watanni masu zuwa a cikin yawan mafarke-mafarken da yake yi, amma idan ya sanar da mutanen garinsu sai su yi masa kallon mahaukaci.

Kullum idan ya ba su labarin wani al’amuran da za su faru sai ‘yan ƙauyen su ɗauke shi marar hankali, hakan sai ta sa ya ji ba zai iya zama cikin su ba, sai ya koma cikin kogon bishiyar Kuka wanda yanzu haka ya yi tsawon shekaru biyar yana kwana a cikinta.

 

Za a ji ƙarin bayani a rahoton mu na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here