Isa Ashiru Kudan Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Jam’iyyar PDP Kaduna

0
257

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Maƙarfi da Kudan a majalisar wakilai, Alhaji Isa Ashiru Kudan, Sarkin Bai Zazzau ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP Jihar Kaduna a matsayin wanda zai rike tutar tsayawa takarar neman Kujerar Gwamnan Jihar a karkashin inuwar Jam’iyyar.


Zaben wanda ya gudana a daren ranar laraba a dakin taro na filin wasa Ahmadu Bello (ABS) dake Kaduna, an gudanar da shi ne ba tare hayaniya ko tashin hankali ba yayin da wakilan Jam’iyyar masu zaben yan takara suka kada Kuri’unsu bayan tantancewa.

Alkaluman sakamakon zaɓen sun nuna cewar Chiroman Kudan, Honarabul Isa Ashiru Kudan ya samu kuri’u mafiya rinjaye inda ya doke abokan takarar shi da samun kuri’u 414.

Tuni wasu daga cikin abokanan takarar tashi suka amince da kayen har suka miƙa sakon taya shi murna bisa ga nasarar da ya samu.

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani wanda ya samu kuri’a biyu rak a zaɓen ya wallafa sakon taya murna ga Isa Ashiru Kudan da kuma mika godiya ga wakilan Jam’iyyar da suka zaɓe shi ba tare ya basu ko sisi ba.

Leave a Reply