IPOB ta hallaka ‘Yan sanda 2, Farin hula1, tare da ƙone gawarwakin mutane a Anambra

0
397

Daga Fatima Gimba, Abuja

Wasu gungun ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra ne, IPOB sun kashe ‘yan sanda biyu da farar hula ɗaya a ƙaramar hukumar Amukabra Achalla Awka a jihar Anambra.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga ya bayyana lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a Awka, yace an kashe mutanen uku ne bayan da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su a yayin da suke kokarin ƙwato wata mota da suka sace.

Mista Ikenga, mataimakin sufeton ‘yan sanda ya ce lamarin da ya faru a ranar Juma’a 15 ga watan yuli, ‘yan sandan sun kai farmaki ne, inda bisani aka gano ‘yan ta’addan sun kashe biyu ciki harda farar hula, mota tare da ƙona gawarwakin su.

Rundunar ‘yan sandan ta na kan aikin ƙwato wata mota kirar Toyota Sienna da Space wagon da aka sace a ranar 9 ga watan Yuli, a unguwar Oye-Agu Abagana.

“Jami’an ‘yan sanda hudu ne suka tsere daga harin kwanton ɓauna, yayin da ‘yan sandan biyu da na’urar bin diddigin motar suka samu nasarar kama su.

“A yayin kai farmakin, ‘yan sanda sun kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar tare da lalata sansanoninsu guda uku.

“Abin takaici, wasu daga cikin ‘yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga, tuni suka kashe wadanda suka yi garkuwa da su tare da ƙona gawarwakin su.

“An gano gawarwakin ‘yan sandan biyu da aka kashe da kuma wani farar hular, kawo yanzu an ajiye su a dakin ajiyar gawa, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ‘yan sanda a yankin domin zakulo ‘yan kungiyar da suka gudu,” inji shi.

Kakakin ‘yan sandan kuma ya ce; an yi nasarar kwato kokon kan mutum daya, rokoki guda biyu da aka yi a gida, bama-bamai na RPG.

Sauran abubuwan da aka ƙwato sun hada da; Doguwar bindigar ganga guda daya, sarkar harsashi mara komai, Toyota Sienna daya, Mercedes Benz Formatic Jeep daya da silinda guda biyu.

Ya kuma ƙara da cewa, ƙungiyar ta samu kama manya-manyan miyagun kwayoyi iri-iri, beret na ‘yan sanda daya da bel.

Kazalika sanarwa ta rawaito cewa; kwamishinan ‘yan sanda, Echeng Echeng, ya jajantawa iyalan fararen hula da ‘yan sanda da aka kashe.

A cewar sa, CP ya bayyana lamarin a matsayin wani misali na kasada da sadaukarwa da ‘yan sanda ke yi a cikin babban aiki na yi wa kasa hidima da kuma kare kasa.

Don haka CP ya tabbatar wa mutanen Anambra kan kokarin da ake yi na sake kwatowa da mallake duk wuraren jama’a da ‘yan ta’adda suka mamaye a jihar.

Leave a Reply