IMWON Ta Karrama Umar Tata Da Lambar Yabo Na Islama

0
444

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

WATA kungiyar da ke taimakawa mata da Marayu ta (IMWON), ta karrama Alhaji Umar Abdullahi Tsauri Tata bisa ganin irin namijin kokari da yake da cancantar zama mutumin da ya ke cikin al’ummar dake kyautata mata da Marayu a fannin rayuwa inganta rayuwar Jama’a a cikin addinin musulunci.

Da yake jawabi jim kadan bayan bayan amsar Kyautar karramawar a Kaduna, Abdullahi Tata, ya bayyana farin cikinsa bisa wannan karamcin da Kungiyar ta IMWON ta yi masa ta hanyar nuna cancantarsa da bashi wannan kyautar girmamawa ta lambar yabo ta fuskar addinin Islama bisa yaba wa da irin Kokarin da yake a cikin al’umma.

Tata, ya ci gaba da cewa shi da kansa ya na matukar jin dadin aikin taimakawa Jama’a a koda yaushe don haka ya na kira ga dukkan masu hannu da shuni da su rika taimakawa Jama’ar da suke bukatar taimako a cikin al’umma.

“Kuma ni duk abin da nake aiwatarwa ga Jama’a, ina yi ne domin Allah ba domin wani ko wasu su ce an burge ba”.

Tun da farko, Amirar kungiyar Malama Rabi’ah Sufuwan, ta bayyana irin kokarin da Umar Abdullahi Tata ke yi wa dimbin masu bukatar taimako da cewa shi ne dalilin da ya sa suka ga dacewar bashi wannan lambar karramawar.

“Akwai wata Garkuwar da na so a ba Tata a wannan wuri amma saboda har ya zuwa wannan lokacin ba a kammala kera Garkuwar yadda ya dace ba don haka sai nan gaba za a bashi ita in Allah ya so, domin ayyukan taimakawa jama’a da Tata yake yi su na amfanar dukkan al’umma baki daya, saboda haka muke farin cikin bashi wannan lambar karramawar”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here