Ban Tsaya Takarar Kujerar Sanata Ba – Daraktan ITF

0
310

Daga, Isah Ahmed, Jos.

DARAKTA Janar na Asusun horar da Masana’antu na Kasa (ITF), da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, Sir Joseph Ari ya bayyana cewa masu kokarin bata masa suna ne, suke yada manyan hotunansa da ke nuna cewa ya fito neman takarar kujerar Sanata.

Sir Joseph Ari ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da ‘Yan jarida a Cibiyar ‘Yan jaridu da ke garin Jos.

Acewarsa, a halin da ake ciki yanzu, wasu bata gari suna nan suna manna hotunansa da ke dauke da bayanin cewa ya fito neman takarar kujerar Sanata da kuma hotunan wasu masu takarar neman shugabancin Jam’iyyar APC na Kasa da cewa yana goyan bayan wadannan ‘yan takara.

Ya ce “na gano cewa wadannan bata gari, sun shirya zasu je wajen da za a gudanar da babban taron zaben shugabancin Jam’iyyar APC na Kasa, su manna wadannan hotuna da niyar bata mun suna.”

“Ina kira ga al’umma kan su yi watsi da wadannan bata gari da suke kokarin bata mani suna. Kuma ina son na sanar da duniya cewa bana neman takarar kowace kujera ta zaben siyasa. Ni na mayar da hankalina ne kan aikin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dora mani na shugabancin Asusun horar da masana’antu (ITF) don koyawa matasan Najeriya sana’o’i domin su sami abin dogara da kansu.”

Leave a Reply