Hukumar Kwastan Shiyyar Kano / Jigawa Ta Yi Sabon Shugaba

0
307


Daga Rabo Haladu 
Shugaban hukumar Kwastan ta kasa Kanar Hameed Ibrahim Ali (Mai murabus) ya bayyana sunan M A Umar,a matsayin sabon shugaban hukumar Kwastan Shiyyar Kano/Jigawa.
A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai Mai dauke da sa hannun shugaban hukumar, ya ce hukumar ta nada sabbin shugabannin hukumar na jihohi guda 37 a fadin kasar Nan wadanda Kuma tuni hukumar ta turasu jihohin  domin fara gudanar  da ayyukan Hana fasa kwauri a fadin yankunansu baki daya.
M A Umar, Wanda shine ya maye gurbin tsohon shugaban hukumar na Shiyyar Kano/ Jigawa, Suleiman Pai Umar, Wanda hukumar ta mayar dashi hedikwatar hukumar dake Abuja domin ci gaba da aiki.
Umar, wanda aka bayyana shi a matsayin jami’in hukumar Kwastan mai jajircewa wajen yaki da ‘yan fasa kwaurin haramtattun Kaya daga kasar waje zuwa Nijeriya zai jagoranci hukumar ne domin kawo sauyi akan wasu  matsalolin da suka addabi Shiyyar.
Kanar Hameed Ibrahim Ali, ya bukaci sabbin shugabannin da su zama masu taka- tsan- tsan wajen kaucewa abubuwan da za su kawo musu cikas a yayin gudanar da ayyukansu.
Hakazalika, sanarwar tace duk sabbin shugabannin su 37 zasu  fara aiki nan take tun daga ranar 8 ga watan fabrairun wannan shekarar.
Shi ma babban jami’n Hulda da jama’a na hukumar Kwastan ta kasa Joseph Attah, shi zai jagoranci hukumar Kwastan ta Jihar Kebbi wanda ya maye gurbin tsohon shugaban hukumar na Jihar Hafis Kalla wanda shi ne aka mayar da shi hedikwatar hukumar Kwastan ta kasa domin ci gaba da aiki.
Sanarwar kuma ta ruwaito Hameed Ibrahim Ali yana musu fatan alkhairi bisa wannan matsayin da suka samu inda ya ce ya zama wajibi a kansu da su Samar da yanayi Mai kyau wajen ciyar da hukumar dama kasa gaba ta bangarori da dama.

Leave a Reply