Haruna AG, Ya Koma Jam’iyyar PDP Domin Yin Takarar Gwamnan Kaduna

0
408

Daga; USMAN NASIDI Da MUSTAPHA IMRANA, Kaduna.

TSOHON Dan takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna a Jam’iyyar CPC, APC da SDP wanda yake tsohon babban akanta Janar Gwamnatin Jihar da ya fi kowanne dadewa a kan mukamin, Alhaji Dokta Haruna Yunusa Saeed Kajuru, ya sauya sheka ta hanyar komawa Jam’iyyar PDP.

Dan takarar Kujerar Gwamnan Jihar, ya bayyana kudirinsa ne a yayin wani gangamin komawarsa Jam’iyyar PDP wacce ya bayyana a matsayin gida da kuma bayyana ra’ayinsa na tsaya takarar neman Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna a ranar talata a sakatariyar Jam’iyyar da ke NDA Kaduna.

Da yake jawabi a wajen taron, Haruna Saeed (AG), ya bayyana cancanta, kokari, iya aiki da sanin ciki da wajen Jihar a matsayin ma’aunin da za a yi amfani da shi wajen zabe shi a matsayin dan takarar Kujerar Gwamnan Jihar.

Ya ce “kamar yadda na Sani ni ne a kan gaba wajen ganin Jam’iyyar APC ta Kafu sosai a Jihar Kaduna, har aka samu nasarar da ake takama da ita a yanzu amma kuma bisa wadansu dalilai a halin yanzu na koma asalin gidana na wacce ta ke PDP wanda tare da ni aka kafa ta kuma ba rike mukamai tare da yin ayyukan ci gaban rayuwar Jama’a da dama a cikin ta”.

“Ni ne ma’aikacin da ya fi kowa dadewa a kan kujerar babban akanta Janar a Jihar Kaduna domin na shekara Goma sha daya (11) da ba a ta ba samun wanda ya samu damar yin hakan ba, na kuma yi aikin karantarwa tun daga Firamare, sakandare zuwa Jami’a na yi aikace-aikace da dama da suka hada da shugaban kamfanin zuba jari da hukumar NAITI inda na zama shugaba baki daya a Najeriya”.

Ni ne dai wanda aka Sani ina nan ban canza ba sai ci gaban da na yi, kuma na gina makarantar sakandare tun daga matakin aji uku zuwa babbar sakandare na ba Gwamnati kyauta na kuma gina makarantun Islamiyya da masallatai duk domin taimakawa bayin Allah.

Acewarsa, ko a halin yanzu da akwai abubuwa da dama da zai yi wa Jihar Kaduna domin a samu ci gaban da kowa ke bukatar samu don su ke da masaniya a kan wurare da dama wadanda suka hada da lunguna-lunguna a cikin birane da karkara.

Hakazalika, ya koka bisa irin yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ke aikin tituna a garin Kaduna da kuma yan kadan a Zariya da Kafanchan wanda hakan da sauran abin dubawa domin kamar shi da ya fito daga kauye har yanzu su na jiran ayi masu aiki, domin tun daga Gwantu zuwa Fala zuwa yankin Dogon Dawa har karshen birnin Gwari a Jihar Kaduna duk ko’ina sun san haka, balantana shi da ya yi aiki a matsayin makogwaron Jihar Kaduna ta fuskar kudi wadda kowace ma’aikata sai ta zo ofishinsa.

Yayin da mayar da martani ga Dan takarar, Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Mista Felix Hassan Hyet, ya bayyana Jindadinsu bisa ganin tsohon dan Jam’iyyar da magoya bayansa sun yi mubayi’a, kana sun dawo Jam’iyyar ta su ta PDP wacce ya bayyana a matsayin mai albarka da nasara.

Shugaban ya kara da cewa yin hakan na nuni da cewa wata dama ce a gare da zasu iya samun nasarar kwace duk wasu kujeru daga hannun Jam’iyyar adawa mai mulki idan har sun yi dacen samun mutane yan takara na gari, ko da ita Jam’iyyar PDP ba zata yiwa kowa karfa-karfa ba face sai abin da mutane suka zaba yayin zaben fidda gwani.

A karshe, ya shawarci Haruna Saeed (AG) da sauran yan takarar da su san cewa Mulkin na Allah ne kuma su san irin kalaman da zasu rika amfani da su domin sun zama majibantan yan uwan juna saboda haka kowani Dan takara ya yi kokarin ganin cewa ya kiyaye duk wani abun da zai haifar da wata matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here