Harin Jirgin Kasa: Uba Sani Ya Nemi Hukumomin Tsaro Su Gaggauta Sauya Dabaru

0
308

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SANATA mai wakiltar Shiyyar Kaduna ta tsakiya Malam Uba Sani, ya yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gaggauta sauya dabaru domin yakar ta’addanci, ‘yan fashi da sauran matsalolin rashin tsaro a fadin Najeriya, musamman a Jihar Kaduna.

A wani kudiri da aka gabatar a Majalisar Dattawan game da harin da aka kai a daren Litinin wanda ya jawo cece-kuce, Sanatan mai wakiltar Shiyyar Kaduna ta tsakiya ya bayar da umarni na 41 da 51 da suka dace da neman izinin majalisar dattawa ta gabatar da kudiri kan hare-haren ‘yan bindiga dake hanyar Abuja-Kaduna da kuma wasu sassan Jihar.

Dan takarar Gwamnan Kaduna a zaben 2023 mai gabatowa ya koka da yawaitar hare-haren da ake kaiwa kauyukan da ba su jin dadin ganin hakan, wadanda ya ce al’ummar suna fuskantar azabar da ba za a iya misalta su ba, hasarar rayuka da ababen more rayuwa.

Ya bayyana cewa an kashe sama da mutane 50 tare da yin garkuwa da wasu 100 a cikin kwanaki uku a kauyukan da ke fadin kananan hukumomin Igabi da Giwa wanda ya ce sun wani yanki ne a mazabar sa na shiyyar Kaduna ta tsakiya.

Sanatan ya ce a tunaninsa idan aka ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda zaman lafiya zai dawo, amma abin takaici, ya koka da cewa sabanin yadda lamarin ya kasance na ta’addanci – abubuwan da ke da alaka da su da suka yi sanadin asarar rayuka da kuma kara yawan ‘yan gudun hijira.

Ya yi mamakin yadda mutum mai hankali zai dana nakiya a jirgin fasinjoji su kama harba harsasai a cikin mutane, ciki har da mata da yara da kuma sace wasu dari ba tare da tausayi ba.

Sanatan ya kalubalanci hukumomin tsaro da su dauki ingantacciyar hanyar yaki da ta’addanci ba ta hanyoyin da aka saba amfani da su ba, inda ya bayyana cewa dole ne a dakatar da asarar rayuka ta hanyar da ta dace ta yadda ‘yan Najeriya za su rika tafiye-tafiye da gudanar da sana’o’insu na halal ba tare da tsoro ko tsangwama ba.

Ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, yana mai rokon Allah ya jikan su kuma yi addu’ar Allah ya bayyana wadanda aka sace cikin gaggawa.

Leave a Reply